Arewa Plus

Arewa Plus

Share

Photos from Arewa Plus's post 30/03/2026

Tsoron Dan takarar Gwamnan jahar jigawa a tutar jam'iyar NNPP a zaben 2023 ya bada sanarwar fitarsa daga jam'iyar NNPP ya shiga jam'iyar ADC.

01/10/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Lawan Triumph daga yon wa'azi

Majalisar Shura da gwamnatin Kano ta kafa ya sanar da dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa'azi.

A wani taron manema labarai da Sakataren majalisar, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi a yau Laraba, ya ce an dakatar da Malam Lawan ne domin bashi damar ya zo gaban majalisar ya kare kan sa daga zarge-zargen da ake yi masa na yin kalaman ɓatanci ga Ma'aiki.

A cewar Sagagi, an dakatar da Malam Lawan har sai an kammala bincike da jin ta bakin sa a matakin Majalisar ta shura.

Ya kuma yi kira ga ƴan siyasa da su guji tsoma baki a batun, inda ya bukaci da a kyale kwamitin ya kammala aikin sa.

Sagagi ya tabbatar da cewa Majalisar za ta yi aiki tsakani da Allah ba tare da don rai ko rashin adalci ba.

25/09/2025

Ana zargin matashi Mutawakkil, wanda aka fi sani da Tony, da kashe kakanninsa ta hanyar caka musu wuka a unguwar Kofar Ruwa da safiyar yau.

Rahotanni sun nuna cewa bayan kisan, matashin ya yi yunkurin tserewa ta shiga wani gida, amma al’ummar unguwar s**a yi ƙoƙarin cafke shi. Daga bisani jami’an Hisbah na Dala s**a iso wajen, s**a mika lamarin ga ’yan sanda, waɗanda s**a tabbatar da cafke shi tare da kai shi ofishinsu.

Kakannin nasa kuwa an garzaya da su asibiti domin duba lafiyarsu, sai dai daga bisani rundunar ’yan sanda ta Kano ta tabbatar da rasuwarsu.

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce za a fitar da ƙarin bayani nan gaba.

Arewa plus

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address


Kano