Bashir BARAU

Bashir BARAU

Share

16/09/2022

KANMU A WAYE YAKE AMMA FA 'YAN UWA MU KARA HATTARA:
1. A kokarin makiya musulunci na dagula lamuran musulmin arewacin najeriya ta hanyar amfani da kafafen sa da zumunta, da farko suna amfani da banbance banbancen dake tsakanin musulmi suna yin kutse suyi zagi da aibata wani bangare a matsayin su musulmi ne 'yan wani bangare, kuma da daga nan sai su goce su kyale wawaye suyi ta s**a da aibata juna.
2. A yanzu kuma ganin hakansu yaki cimma ruwa shine s**a fito da wata dabara amma a irin nasu tunanin, wato ta amfani da arna a matsayin su Hausawa ne ko ma musulmai da kuma wawaye 'yan babu ruwansu da addini,, suna amfani da yanayin da ake ciki na rashin tsaro suna yada maganganun raba kan Hausawa da Fulani har ta kai suna zagin Shehu Usmanu dan Fodio wai ya zalunci Hausawa. To yanzu kuma kiyayyar tasu da arnancin nasu sun gagara boyewa, sun fara fito da manufarsu ta dirarwa addinin musulunci kai tsaye, yanzu suna fassara wasu shibhohi wato labaran karya da aka rubuta da harshen turanci don bata musulunci a idon arna, suna yadawa kan wai Larabawa sun bautar da 'yan Afrika, sun tursasasu yin musulunci ta dole, daga nan zakuji sunyi gaba in sun sami hali.
Abin tsokaci anan shine yakamata musan cewa mu al'ummar musulmi hausa/fulani kanmu a waye yake wajen gane irin wadannan shegantakun, amma kuma dole ne muyi hattara da sanya ido tare da taka tsantsan dangane da bibiyar irin wadannan rubuce rubuce, musamman ga masu zafin akida. Allah ya kara kare musulunci da al'ummar musulmi daga sharrin makiya, Allah ya karawa Annabi daraja.

31/08/2022

KIRA GA 'YAN UWA TALAKAWA:
1. Tabbas talaka ya wahala a hannun shugabanni ' Yan siyasa.
2. To yanzu ga lokacin sake zaban shugabanni ya karato kada mu yarda mu dawwamar da kanmu cikin wahala, mu tsaya muyi tunani a karan kanmu kada mu dogara da tunanin wasu kawai.
3. Bai kamata mu ci gaba da zaben shugabanni da zasu rika wahalar damu ba.
4. Kada a yaudaremu da abin da bazai raba mu da talauci ba wajen yin zabe.
5. Kada soyayyar jam'iyya ko wani dan siyasa ya sanya mu yin zabe da ka.
6. Ya kamata musan farashinmu mu talakawa, ma'ana abubuwan da muke da bukata, su kuma 'yan siyasa muji irin tayinsu garemu, ma'ana me zasu iya yi mana daga bukatunmu, amma kada kawai muce sai wane sai wane saboda kawai dan jam'iyya kaza ne ba tare da yarjejeniya da alkawarin abin da zai yiwa talakawa ba. Mun dai san abin da ya faru jiya. Allah yasa mu fahimta

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Gwale Ward
Kano