Daily Hustle Dose
17/04/2026
GASKIYAR BUƊE MASHIGAR HORMUZ........
Wata majiya mai kusanci da Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran ta bayyana wa kafar yaɗa labarai ta Iran wasu bayanai game da buɗe mashigin Hormuz na ɗan lokaci — k**ar yadda Fars News Agency ta ruwaito.
Majiyar ta ce akwai sabbin bayanai kan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da Amurka a lokacin tsagaita wuta na makonni biyu, dangane da mashigin Hormuz.
A cewarta, tun farkon shirin tsagaita wutar da Pakistan ta shiga tsakani, an tsara cewa Iran za ta bari wasu jiragen ruwa su rika wucewa kowace rana.
Sai dai bayan ba a aiwatar da tsagaita wutar a Lebanon ba, kuma ba a amince a haɗa HZL cikin yarjejeniyar ba, Iran ta dakatar da yarjejeniyar barin jiragen ruwa su ratsa mashigin.
Majiyar ta ce Iran ta gindaya sharuɗɗa uku domin jirage su ratsa mashigin Hormuz:
1. Jiragen dole su kasance na kasuwanci kawai; ba a yarda da jiragen yaƙi ba, kuma jirgin ko kayan da yake ɗauke da su ba su da alaƙa da ƙasashen da ake kallon su a matsayin maƙiya Iran, (Kamar Amurk@ da Muzra’ila).
2. Dole jiragen su bi hanyar da Iran ta ayyana.
3. Dole a daidaita wucewar jiragen da sojojin Iran masu kula da yankin; k**ar yadda CENTCOM ta taɓa tabbatar da ikon da dakarun Iran ke da shi a mashigin kafin yaƙin ya fara.
— Muhammad Balaa Afuwaa
13/04/2026
Wani jami'i ya turomin cewa
Kasuwar Jilli da aka kai hari, gwamnati ta rufe wannan kasuwar sama da shekaru biyar (5)
Kamin sojojin sama s**ai wannan harin, sai da s**a tabbatar da ganin mayaƙan Boko Haram acikin wannan kasuwar da motocinsu da mak**ai
Menene ra'ayinku akan wannan saƙon?
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano