Inter mian
16/11/2025
"Ba don Burkina Faso kawai muke yaƙi ba, muna yaƙi don Afirka da mutuncin Baƙar fata" — Traóre
Shugaban Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, ya gana da Afrodescendants a ranar Juma'a 7 ga Nuwamba 2025 a Ouagadougou a ƙarƙashin shirin "Bienvenue chez vous" wa'inda s**a sake nuna goyon bayansu gare shi da niyyar zuba jari da zama a ƙasar cikin ɗa'a da mutunci.
Traóre ya bayyana su a matsayin “Jakadu 700 na Burkina Faso”, inda ya sanar musu da cewa an cire sharadin kuɗi wajen samun katin zama na dindindin a ƙasar.
Ya jaddada cewa gwagwarmayar da Burkina Faso ke yi ba don ƙasarsu kaɗai ba ce, illa dai gwagwarmaya wadda ya ayyana a matsayin 'yantar da Baƙar fata gaba ɗaya, da kare mutuncin Afirka da walwalar al’umma.
"Muna yaƙi don Afirka. Muna yaƙi don mutuncin Baƙar fata. Muna yaƙi don jin daɗin al’ummarmu," in ji shi.
14/11/2025
Bayan gudanar da Sallolin Neman Ruwan Sama wato Salat al-Istisqa a jiya a Masallatan Harami, Masjid Al-Haram da Masjid An-Nabawi, yau rahama ta biyo baya, inda ruwan sama ya sauka a garuruwan Makkah da Madina.
Sallar Istisqa, wacce aka yi a safiyar jiya bisa umarnin Sarkin Saudiyya, ta tara dubban musulmi domin roƙon Allah ya saukar da ruwa saboda matsanancin fari da yankin ke fama da shi. A yau, rahama ta bayyana cikin sautin ruwan sama da ya sauka cikin nutsuwa a harabar masallatan biyu.
Masu ziyara da ma’aikatan masallatan sun bayyana farin cikinsu, suna kallon wannan a matsayin amsar addu’a da kuma alamar albarka ga ƙasar Saudiyya.
Shin a ganinku wannan ruwan sama amsa ce kai tsaye ga addu’ar jiya?
📷/: Source/: Haramain [X]
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Nigeria Kano
Kano