Hadisai zallah

Hadisai zallah

Share

26/01/2022

11-Annabi (s) yana cewa:”Abubuwa biyu sun halakar da mutane,tsoron talauci,da neman suna”.

12-Annabi (s) ya ce: “Abubuwa biyu basa haduwa a musulmi, rowa da mummunan hali”.

13-Annabi (s) ya ce: “Bai yi imani ba,mutumin da ya kasance yana da rowa,ko hassada,ko ragwanci,mumini bai kasance wa mai ragontaka,ko kwadayi,ko kwauro”.

14-Annabi (s) ya ce:”abubuwa 3 darajoji ne,3 kaffarori ne,3 masu halakarwa ne,3 masu tseratarwa ne.

Darajojin su ne:yada sallama,ciyar da abinci,sAllah da dare lokacin da mutane ke bacci.

Kaffarorin su ne:kyautata alwala lokacin sanyi,tafiya dare da rana zuwa masallatai da kiyaye jam’o’i.

Amma 3 masu halakarwa:kwauro abin bi,bin son zuciya,da tinkahon mutum ga kan sa.

Masu tseratarwa kuma:tsoron Allah a asirce da fili,da tsakaitawa a halin yalwa da talauci,da kalmar gaskiya a halin yarda ko fushi”.

15-Annabi (s) ya ce:”abubuwa 3,duk wanda s**a kasance a cikin sa Allah zai aura masa Hurul ini yanda ya so:Hadiye fushi,dauriya kan Takubba saboda Allah da mutumin da ya sami iko kan dukiyar haram sai ya barta saboda Allah”.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Culinary Team

Attire

Telephone

Website

Address


Sharada
Kano
1111