Aminchi Tv

Aminchi Tv

Share

31/05/2026

Kasar Korea ta Kudu ta bayyana cewa ta gudanar da tattaunawa da Japan kan wata sabuwar yarjejeniya da za ta tanadi yadda kasashen biyu za su rika musayar tallafin soji da kuma jigilar kayan aikin tsaro a tsakaninsu.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan mataki na daga cikin kokarin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin tsaro, musamman a yankin Asiya da ke fuskantar kalubalen tsaro daga wasu bangarori.

Korea ta Kudu ta kara da cewa har yanzu ana ci gaba da nazari kan batun, kuma ba a kammala cimma matsaya ta karshe ba.

31/05/2026

Wasu da ake zargin ƴan daba ne sun tarwatsa taron shugabannin jam'iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki a cibiyar taruka ta A-Class Event Centre da ke Abuja.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan shugabannin ɓangaren jam'iyyar sun koma wurin domin ganawa da jami'an tsaro da aka girke a wajen.

Tun da farko, ɓangaren PDP na Kabiru Turaki ya gudanar da Babban Taron Musamman na Ƙasa a ofishin sa da ke Area 10 a Abuja, inda ya amince da tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen 2027.

Shugabannin jam'iyyar sun bayyana cewa sun koma ofishin Area 10 ne bayan jami'an tsaro sun toshe hanyar shiga cibiyar taron ta A-Class Event Centre, wadda aka shirya gudanar da taron a cikin ta.

Bayan kammala bikin amincewa da Jonathan, shugabannin jam'iyyar sun koma cibiyar taron domin abin da s**a bayyana a matsayin tattaunawa da jami'an 'yan sanda da ke wurin.

Sai dai jim kaɗan bayan Kabiru Turaki ya kammala jawabin sa, wasu matasa da s**a iso cikin motocin bas guda biyu dauke da manyan sanduna s**a kai farmaki kan jami'an jam'iyyar yayin da suke komawa motocin su.

Harin ya tilasta wa shugabannin jam'iyyar, 'yan jarida da sauran mahalarta taron tserewa domin tsira da rayukansu.

Daga bisani, jami'an 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun dawo da zaman lafiya a wurin.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Kano