Akcccosa 2018 Chapter
01/03/2024
Bana mantawa a secondary school ɗin mu Akcccosa 2018 Chapter lokacin ina deputy ɗin Sadiq Hussain Lameen a matsayin Head of Students an samu canjin sabon director na makaranta. Da yazo sai ya ga perfects suna dukan ɗalibai kuma suna bada punishment iri-iri k**ar picking, shara da sauransu idan sun yi laifi. Lallai wani sa'in prefects muna wuce gona da iri a hukunci, saboda haka sabon director ya hana mu ko wani irin punishment saidai mu yi reporting ga malamai. Yayi wannan hanin publicly a gaban ɗaliban da muke jagoranta. Hakan ya jawo raini a tsakanin mu da su da karya doka, lateness da inappropriate dressing s**a ƙara ta'azzara. Da muka ga haka sai muka zauna meeting iya mu perfects muka yanke shawarar cewa ko a yi reinstating ɗin power ɗin mu na da da sharaɗin zamu yi regulating wuce gona da iri da wasun mu suke yi ko kuma idan ba'a yarda da wannan mu ajiye hulunan mu na muƙami gabaɗaya mu bar yaran su yi abinda s**a ga dama dan ba zamu juri muna leading kuma muna ganin yadda aka sakar musu mara suyi fitsara ba. Dan ba mu ga yadda za'a yi mu tabbatar da doka da order a cikin mutum sama da dubu biyu (iya maza) mu ƙasa da talatin ba tare da punishment ba, muna reaching inda hannun teachers din baya iya zuwa saboda mune idon su a kan ɗaliban. Without us they cannot keep the school in order.
Da muka zauna meeting da management ɗin makaranta muka faɗi condition sai wani malami daga cikin su (ba zan faɗi suna ba) ya ce idan muka yi hakan mun yi disrespecting din makaranta ne. Kuma idan muka ajiye muƙami mun kori kan mu daga makaranta. Akwai malamin mu na mathematics Sir Maikuɗi Inusa, ya bamu haƙuri akan yadda aka yi sanctioning ɗin mu publicly kuma ya bamu shawara akan cewa mu dinga cizawa muna hurawa, dan ƙarfin bulala ba zai iya controlling ɗin wannan population ɗin ba dole sai da siyasa. Haka muka tashi daga wannan zama ba'a bamu abinda muka nema ba kuma muka haƙura da ajiye hula. Amma fa daga kan mu ba'a sake samun perfects waƴanda s**a yi keeping ɗin ɗaliban makarantar In-check ba saboda wannan tsarin.
Tabbas a aiki irin na tabbatar da doka da order ana wuce gona da iri kuma wasu daga jami'an Hisba suna wuce gona da iri wajen keta hakkin Ɗan Adam wasu lokuta a ayyukan su amma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf bai kyauta ba da yayi wannan gyara publicly. Hakan zai kashewa commander ɗin Hisba da ma'aikatansa morale. Tunda shi ya naɗa shi sai su zauna close door meeting su tattauna akan gyara wannan matsalar baki alaikum ba sai an ji ba. Daɗin daɗawa gwamna yayi kuskuren bawa wannan yarinya relevance saboda ta yi masa campaign lokacin siyasa har take nuna garin nasu ne zasu yi abinda ya ga dama bayan ya samu nasara. Bai k**ata ya bata muhimmanci har ya karrama ta a idon dunya ta hanyar karɓar ta hannu bibbiyu lokacin da ta kai masa ziyara wadda a kan ta ake ta wannan cece-kuce kuma ita ce ummul aba'isin wannan taqaddama. Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya sauka daga muƙami ne saboda kare mutuncin sa saboda wannan nuna rashin matsayi nasa da gwamna yayi subtly, ko shi gwamnan ya sani ko bai sani ba ko willingly yayi ko unwillingly wannan ya taɓa shaksiyyar power ɗin commander Kuma this is a political and administrative blunder, wanda ba haka aka so ba. Bayan faruwar wannan al'amari ya muke zaton Commander da jami'an sa zasu yi aikin da ya k**ata cikin karsashi bayan an nuna wa mutanen gari da ashararai iyakar sa ta hanyar da bata dace ba?
Amma da malam yayi haƙuri ya jure ya zauna da ya fi, saboda bamu san wa za'a a kawo gaba ba, dukda muna fatan alkhairi muna tsoron a kawo wanda bai cancanta ba. Idan hakan ta faru al'amuran hani da mummuna da umarni da mai kyau zasu jagule a Kano. Da malam yayi wannan sacrifice ɗin ya gyara ɓarakar da ya fi. Muna tsoron hakan ya buɗe wata ƙofar ɓarna Allah ya kiyaye.
Aliyu Ibrahim Haidar ✍️
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
P. M. P 3117 Aminu Kano Way
Kano