DAN MANYA
14/12/2025
Muhimmiyyar Sanarwar Ga Masu Neman Aiki!
Darul Aytam Academy Bauchi (Makarantar Marayu na Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum) na gayyatar Waɗanda suke buƙatar aiki, masu jajircewa da nagarta don cike guraben aiki kamar haka:
1. Shugaban Makaranta (Principal)
2. Jami’in Gudanarwa (Administrative Officer)
3. Ma’aikacin Ajiya (Store Officer)
4. Malamai (Dukkan Fannonin Karatu)
5. Malaman Qur’ani
Sharuddan Da Ake Son Mai Neman Aiki ya cika:
- Ya kasance mai ladabi, amana da tsoron Allah
- Ya Kasance mai Kishi da son cigaban Makaranta.
- Ya kasance mai ƙoƙari da himma
- Ya kasance ya iya mu’amala da yin aiki tare da wasu
- Ya kasance ya damu da marayu da kokari wajen farfaɗo da rayuwarsu
- Ya kasance da takardun da s**a dace da gurbin da ake nema
1. Shugaban Makaranta
Takardar Shaidan karatu na: B.Ed / B.A Ed / B.Sc Ed ko makamancin haka
Buƙatu na musamman
- Ilimin addini da nagarta
- Ƙwarewa wajen jagoranci da gudanarwa a makaranta
- Iya sa ido kan malamai da tabbatar da ingancin karatu
2. Jami'in Gudanarwa (Admin Officer)
Takardar Shaidan karatu na: ND/HND/B.Sc a fannin Public Admin.
Bukatu na musamman:
- Ƙwarewa wajen tsara bayanai da adanawa
- Iyawa amfani da kwamfuta
3. Ma’aikacin Ajiya (Store Officer)
Takardar Shaidan karatu na: ND/NCE ko makamancin haka
Bukatu na musamman:
- Ƙwarewa wajen kula da kayayyaki
- Iy amfani da kwamfuta (fa'ida ce)
4. Malamin da zai iya Koyar a fannoni Daban Daban (Conventional Subjects)
Takardar Shaidan karatu na: NCE / B.Ed / B.A / B.Sc a fannin da ya dace.
Bukatu na musamman:
- Iya Turanci
- Iya lissafi
- Ƙwarewar koyarwa
- Rijista da TRCN fa’ida ce
5. Malaman Qur’ani
Abun Ake Buƙata: Kammala haddar Qur’ani.
Bukatu na musamman:
- Ƙwarewar haddar Qur’ani da tajweed
- Ƙwarewar koyar da Qur’ani
- Iyawa magana da Larabci fa’ida ce
YADDA AKE NEMAN AIKI:
A tura CV da Takardar Neman Aiki zuwa:
Board of Trustees,
Darul Aytam Academy, Kusa da Masjidud Da’awah, dake Kan hanyar National Open University Bauchi.
Domin Neman ƙarin Bayani sai a Tuntuɓe mu
08149690479 | 0813 344 2461
Za'a rufi Ranar 19/ December/2025
⭕ Waɗanda aka zaɓa kawai za a kira don ganawa.
13/12/2025
Manzon Allah yana da Girma.
Na jima banga hadisin da ya fito da girman Manzon Allah da fifikonsa akan bayi irin wannan Hadisin Abu Zarrin da yake tambayar Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam cewa ya akai ya gane shi Annabi ne kuma har ya sakankance da haka? Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace: “wasu Malaiku guda biyu sunzo min ina wani waje a Makkah, sai daya Malaikan ya sauko kasa, dayan kuma ya tsaya tsakanin sama da Kasa, sai daya Malaikan yake tambayar dayan, wai shine kuwa? Sai dayan ya bashi amsa yace eh. Sai dayan yace toh dauke shi ka auna shi a sikeli da mutum daya aga waye yafi nauyi, sai aka daukeni aka gwadani da mutum daya a cikin mutane, sai nafi shi nauyi. Sai aka sake cewa toh a dauko mutum goma a gwadani dasu a Sikeli, sai aka ga nafi goman nauyi, sai aka ce a dauko mutum dari, sai aka gwada suma na fisu nauyi, sai aka ce a dauko mutum dubu, sai aka ga nafi mutum dubu nauyi, saboda rashin nauyin dubu din ma ina ganinsu suna shawagi akan sikelinsu. Sai dayan Malaikan yace da daya, da zaka auna shi a sikeli da dukkan al’ummarsa da sai ya rinjeta”. Sallallahu Alaihi wasallam.
Allah kayi salati da tsira da Aminci ga fiyayyen Halitta Annabi Muhammad da Iyalansa.
13/12/2025
Duk Mutumin Da Kake Gani Bashi Da Natsuwa, Toh Baya Halartar Wajan Wa’azi Ne. Amma Matuƙar Zai Ringa Zuwa Gurin Da Ake Wa’azi, Toh Allah Zai Bashi Natsuwa
Sheikh Abdurrazaq Yahaya Haifan ( HAFIZAHULLAH )
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Kutama
Kano