Global Community For Human Rights Network

Global Community For Human Rights Network

Share

Photos from Global Community For Human Rights Network's post 20/04/2026

SAKUN TAYA MURNA AURE

An daura auren matashin ɗan jarida daga Radio Dala FM

Ƙungiyar Global Community for Human Rights Network Nigeria

na taya ɗaya daga cikin fitattun ‘yan jarida a fannin labarai na gidan Radio Dala FM dake jihar Kano State, Hassan Mamuda Ya’u, murnar angwancewarsa da aka gudanar cikin farin ciki da walwala.

Ƙungiyar ta bayyana farin cikinta bisa wannan muhimmin mataki da ya ɗauka a rayuwarsa, tare da fatan Allah Ya sanya alkhairi da albarka a cikin wannan aure.

Haka kuma, ana addu’ar Allah Ya ba su zaman lafiya, soyayya mai ɗorewa, fahimtar juna, da zuri’a nagari shi da amaryarsa.
Allah Ya sanya alkhairi, Ameen.

Photos from Global Community For Human Rights Network's post 15/04/2026

GLOBAL COMMUNITY FOR HUMAN RIGHTS NETWORK NIGERIA

TA YABAWA KOTUN SHARI’AR MUSULUNCI TA KADUNA KAN

HUKUNCI MAI ADALCI

Ƙungiyar Global Community for Human Rights Network Nigeria

tana miƙa cikakkiyar yabo da jin daɗinta ga Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kaduna

bisa hukuncin da ta yanke na rusa wata takardar aure da aka tabbatar da cewa ta bogi ce kuma mara inganci.

Wannan hukunci ya nuna ƙwazon kotun wajen tabbatar da gaskiya da adalci ba tare da tsoro ko son zuciya ba.

Hakan ya ƙara tabbatar da cewa har yanzu akwai alkalai masu tsayawa tsayin daka wajen kare mutuncin shari’a da kuma martabar al’umma.

Rahotanni sun bayyana cewa kotun ta yi hukunci a kan batun da ya shafi:

Dr. Ahmad Abubakar Gumi

Mal. Abdullahi Abubakar Goron Namaye

Mal. Umar Sambo (Shahada)

inda aka zarge su da hannu wajen ƙirƙirar takardar aure ta bogi tare da amfani da ita domin tsoma baki a cikin auren Nasir Musa Idris (Albani Agege) da matarsa ƴar Morocco, duk da cewa ba su da wata alaƙa da auren.
A hukuncinta, kotun ta tabbatar da cewa:

Takardar auren ta bogi ce kuma ba sahihiya ba
An ƙirƙire ta ne ba bisa ƙa’ida ba
An haramta amfani da ita gaba ɗaya
An umarci duk mai riƙe da ita da ya miƙa ta nan take

Bugu da ƙari, kotun ta dakatar da duk wata mu’amala da matar da ta shafi wannan rikici, tare da gargadin cewa duk wanda ya saɓa zai fuskanci hukunci mai tsauri.

Tunda fari kungiyar mu tana bin shari'ar tun daga tushe har zuwa yanzu

Ƙungiyarmu tana ganin wannan hukunci a matsayin babbar nasara ga adalci da kuma darasi ga duk wanda ke ƙoƙarin karkatar da gaskiya ko amfani da hanyoyin da ba su dace ba wajen cimma wata manufa.

Haka kuma, muna ƙarfafa wa hukumomin shari’a gwiwa da su ci gaba da bin diddigin gaskiya da tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka samu da laifi ba tare da nuna bambanci ba.

A ƙarshe, muna kira ga al’umma da su mutunta tsarin shari’a tare da guje wa duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya da mutuncin aure.

27/03/2026

ABUN KUNYA NE, ABUN BAN HAUSHI! GA JARIMI ALI NUHU

Abin takaici ne ganin wasu mutane har yanzu ba su fahimci illar kashe ɗan ta’adda ba—ba wai don tausayi ba, sai don hikima da tsaro na ƙasa.

Ina magana ne kai tsaye ga Ali Nuhu da duk wanda yake da irin wannan ra’ayi.

Eh, gaskiya ne—Human Rights ba ta goyon bayan kashe ɗan ta’adda ba.

Amma tambaya ita ce: shin kun fahimci DALILI?

Kashe ɗan ta’adda k**ar kashe maciji ne ba tare da sare kansa ba. Ka kashe guda ɗaya, amma tushen matsalar yana nan daram!
Tambaya ga masu hankali:

Shin waɗannan ‘yan ta’adda suna aiki ne su kaɗai?

Ko akwai MANYAN MUTANE a bayan su‘yan siyasa, masu kuɗi, masu iko—waɗanda ke cin gajiyar wannan ta’addanci?
Idan aka kashe ɗan ta’adda, wa zai tona asirin waɗanda ke ɗaukar nauyinsa?
Ku tuna tarihi: lokacin da aka k**a shugaban Boko Haram, ya fara tona wasu asirai masu girma… amma me ya faru? An kashe shi kafin ya gama magana.

Shin wannan ya kawo ƙarshen Boko Haram ne? Amsar ita ce A’A!
Saboda matsalar ba a sama take ba—a ƙasa take, a ofisoshi take, a hannun masu iko take!
A Nigeria akwai nau’ikan ‘yan ta’adda guda biyu:

Na daji – masu bindiga, masu garkuwa da mutane, masu kashe rayuka.

Na ofis – masu kujeru, masu bada umarni,

masu cin ribar jini da hawaye.

Wadannan na ofis su ne tushen matsala!

Shi ya sa idan aka k**a ɗan ta’adda, sai ka ga an sake shi.

Me yasa?
Saboda ubannin gidansa suna zaune a ofis suna bada umarni!
Amma ina matsalar take?

Mu ne matsalar! Ni da kai!

Ba ma bin diddigi, ba ma tambaya, ba ma neman gaskiya.

Sai mu yi shiru, mu zama bayi cikin ƙasarmu.

Saboda haka: Ina kira ga Ali Nuhu da ya sake duba wannan magana nasa, ya janye ta, domin irin wannan bayani na iya rikitar da jama’a da raunana fahimtar yaki da ta’addanci.

Yaki da ta’addanci ba kashe mutum kawai bane—yaki ne da tsari, da masu daukar nauyi, da masu cin moriya!

02/03/2026

SANARWA TA GAGAWA

(PRESS RELEASE)

GLOBAL COMMUNITY FOR HUMAN RIGHTS NETWORK

Tana Allah wadai da kakkausar murya kan kisan gillar da aka yi wa Jagoran Addinin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Wannan mummunan lamari babban abin takaici ne ga bil’adama, kuma barazana ce ga zaman lafiya da tsaron duniya baki ɗaya. Kashe shugabanni ta hanyar tashin hankali ba zai haifar da mafita ba, sai dai ƙara rura wutar rikici, jini da rashin zaman lafiya a duniya.

Kungiyarmu na kira ga dukkan ƙasashen da suke cikin rikici da su dakatar da tashin hankali, su rungumi tattaunawa, sulhu da hanyoyin zaman lafiya domin kare rayukan fararen hula da martabar ɗan Adam.

Muna kuma kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin duniya da su gaggauta ɗaukar matakan da s**a dace domin hana faɗaɗa rikici da tabbatar da adalci.

Hakkin rayuwa da mutuncin ɗan Adam dole ne su kasance ginshiƙin duk wata manufa ta siyasa ko tsaro.

Allah Ya kawo zaman lafiya mai ɗorewa a duniya.

✍️ Global Community for Human Rights Network

24/02/2026

SANARWAR MANEMA LABARAI

GLOBAL COMMUNITY FOR HUMAN RIGHTS NETWORK NIGERIA

Muna yin Allah wadai da kakkausar murya kan cin zarafin da aka yi wa ɗan jarida Abdulbaki Ali Ahmed Sharifai da ake zargin wani jami’in gwamnatin Jihar Kano, Auwal Sani Rogo (SSR), ya aikata a yayin wani taro na gasar kamun kifi ta Argungu.

Wannan abu ba wai cin mutuncin mutum ɗaya ba ne kawai — hari ne kai tsaye ga ’yancin aikin jarida, ’yancin faɗin albarkacin baki, da dimokuraɗiyya baki ɗaya.

Abin takaici, lamarin ya faru a gaban manyan jami’an gwamnati,

amma har yanzu babu wata hukunci ko neman afuwa daga wanda ake zargi ko gwamnatin Jihar Kano.

Wannan shiru yana nuna rashin mutunta dokoki da kuma ƙoƙarin danne ’yan jarida.

Muna ba gwamnatin Jihar Kano wa’adin

sa’o’i 24 kacal ta:

Daukar matakin ladabtarwa kan wanda ake zargi

Bayar da hakuri a hukumance ga ɗan jaridar

Tabbatar da kariya ga ’yan jarida a jihar
Idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba,

za mu garzaya kotu domin neman cikakken hakkinsa tare da ɗaukar dukkan matakan doka da s**a dace.

Muna kira ga

kwamashina Yansanda jahar Kano da Yak**a ya gudanarda bincike sannan a gabatar da shi a gaban kutu
munada majiya mai ƙarfi kan an shigar da kurafi gaban kwamashina Yansanda jahar Kano amma yaki zuwa gaiyata da aka yi masa saboda karan tsaye akan doka

Wannan ba shi ne karo na farko ba.

Kwanan nan ma an samu cin zarafin ɗan jarida Aminu Halilu Tudunwada. Wannan yana nuna cewa cin zarafin ’yan jarida a Jihar Kano yana ƙara k**ari, abin da ba za mu lamunta ba.

Muna kira ga:

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam

Kungiyoyin ’yan jarida

Lauyoyi da masu rajin dimokuraɗiyya

Al’umma baki ɗaya

da su tashi tsaye domin kare martabar aikin jarida kafin a mayar da shi abin tsoro.

’Yancin Jarida ba laifi ba ne — ginshiƙi ne na adalci da gaskiya.

✍️ Duk wanda ya ci zarafin ɗan jarida, ya ci zarafin al’umma ne baki ɗaya.

Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Kano
700001