Abu Raudah Hausa Tv

Abu Raudah Hausa Tv

Share

13/05/2026

Takardun sakamakon jarrabawa sun kone yayin da gobara ta tashi a Kwalejin Fasaha ta Kano



Wata gobara ta lalata babban dakin karatu na kwalejin fasaha ta Kano wato Kano State Polytechnic, inda ta kone muhimman takardun karatu, bayanan jarabawa, littattafai da kayan aiki a makarantar da ke Kano.

Lamarin ya faru ne ranar Talata, inda gobarar ta shafi manyan sassan dakin karatun kafin jami’an kashe gobara su samu nasarar shawo kanta.

Har yanzu ba a bayyana adadin asarar da aka yi ba.

Rahotanni sun ce daga cikin abubuwan da gobarar ta lalata akwai bayanan jarabawar dalibai, takardun gudanarwa, kayan koyarwa da sauran kayayyaki masu muhimmanci da aka ajiye a dakin karatun.

Lamarin ya haifar da damuwa kan yiwuwar tangardar da zai iya jawo wa harkokin karatu a makarantar.

Hukumomin makarantar da jami’an agajin gaggawa ba su bayyana musabbabin tashin gobarar ba zuwa yanzu, yayin da ake ci gaba da tantance girman barnar da kuma hanyoyin da za a bi wajen dawo da wasu bayanai da kayayyakin da s**a lalace.

Gobarar na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun yawaitar tashin gobara a gine-ginen gwamnati da cibiyoyi daban-daban a fadin Najeriya cikin watannin baya-bayan nan, lamarin da ke kara jawo hankali kan bukatar inganta matakan kariya da tanadin gaggawa.

Daga Daily Nigerian Hausa

29/04/2026

Do Allah jama'a ana cigiyar wannan yaron mai suna Ukasha Musa sunan Mahaifiyarsa Hajara, An kawo Shi daga Kachako.

Ya bar makarantar Fadimatu Bintu Musa Litahfizil Qur'an Na'ibawa Unguwar Kwari ranar Litinin 6/4/2026.

Idan Allah yasa an gan Shi a tuntuɓi wadannan lambobin
08034338023
08060840000
08032398154
Ko miƙa shi ga hukuma mafi kusa.

Don Allah Jama'a a taimaka da yaɗa wannan saƙo 🙏

15/04/2026

An samu 'Sim Cards' guda 28 a wajen Yan Damfara masu muryar tsofi da sunan Malamai ko Aljanu.

~Abdullahi Haruna Kiyawa

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Brigade Gama Quarters. .
Kano