NDC Unity and Progressive Movement

NDC Unity and Progressive Movement

Share

07/06/2026

Yau na sake tabbatar da cewa irin su Datti Assalafiy babu komai a zuciya su sai kiyayya da burin yaɗa farfaganda. Naga yayi posting wani ID card yana maganar wai wannan ne ID card din da Peter Obi yayi wa yan Arewa lokacin da yake kan mulki.

To abun tambaya ina tsohon ID din da kuma kuka rinka posting a lokacin baya a wana ƙungiyar yan Arewa mazauna kudu.

To wannan ID card an samar da shi ne lokacin Peter Obi yana Gwamnan a Anambra ga dukkanin wani dalibi da yake karatu a jami'o'in garin Anambra domin samun damar kulawar lafiya kyauta ba tare da sun biya ko sisi ba.

A wannan lokacin Indai kai dalibi ne kaje ko wane asibiti a Anambra da wannan ID card din za'a duba ka ayi maka abun daya dace a kyauta ba tare da ka biya ko sisi ba.

Ana masa laƙabi da ANIDS (Anambra Integrated Development Strategy).

Photos from NDC Unity and Progressive Movement's post 04/06/2026

HOTUNA CIKIN DARASI
Hoto na farko Unguwar masu kuɗi marasa ƙuri'a GRA Kano.
Hoto na biyu Unguwar Talakawa wato Gayawa masu ɗumbin mutane masu ƙuri'a.

Ana zaman Yar Mowa da Yar Bora a Jahar Kano.

wasu da zaɓe wasu da morewa.

Abubakar Usman Naibi

26/05/2026

Alhamdulillah mu a kungiyarmu ta NDC Unity and Progressive Movement duk wanda ya samu takara zamu tallata shi zamu zabe shi zamusa A zabe shi.

24/05/2026

Idan har da gaske 'Kano First'

To ga Bakano ya fito takarar mataimakin shugaban ƙasa. Ita ce mafi girman kujerar da duk wani Bakano zai yi takararta a zaɓen 2027.

Duk waɗanda s**a fito takarar shugaban ƙasa da mataimakansu babu Bakano a cikinsu. Kuma Kano ce ke basu mafi rinjayen ƙuri'u. Don me yasa zamu gina wasu mu ƙyale kanmu?

A zo a nunawa Kano ƙauna, a zaɓi Bakano.

Want your organization to be the top-listed Government Service in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Kantin Kwari Market
Kano
700280