Juma concept

Juma concept

Share

01/12/2025

Ministan Tsaro Ya Ajiye Aiki

Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya ajiye aikinsa daga mukaminsa nan take.

A wata wasiƙa da ta ɗauki ranar 1 ga Disamba, wadda ya aikawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Badaru ya bayyana cewa ya yi murabus ne saboda dalilan lafiya.

Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin nasa, tare da gode masa bisa irin gudummawar da ya bayar wa ƙasa.

Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da majalisar dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru a cikin wannan makon.

Badaru Abubakar, mai shekaru 63, ya taɓa kasancewa gwamnan jihar Jigawa har sau biyu daga 2015 zuwa 2023. An naɗa shi minista a ranar 21 ga Agusta, 2023, daga Shugaba Tinubu.

Murabus ɗinsa ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya bayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaron ƙasa, inda ake jiran ƙarin bayani kan matakan da gwamnati za ta ɗauka.

18/11/2025

Hoton Dakunan Kwana Na GGCSS Maga, Kebbi inda akai awon gaba da Dalibai 25, da Kuma hallaka Vice Principal

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address


Zoo Road Kano
Kano
8000