Haske Support Foundation
20/04/2026
Haske Support Foundation na ci gaba da haskaka rayuwa da kawo murmushi a zukatan al’umma, musamman marayu da marasa ƙarfi. A ƙarƙashin jagorancin (Uwar Marayu) Hajiya Maryam Shehu Nabage, gidauniyar ta sake nuna jajircewarta wajen ayyukan jin ƙai da tallafi ga masu buƙata.
A wannan karon, gidauniyar ta kai ziyara zuwa wasu sassa na garin Jos, inda ta tallafa wa mutane da dama da ba su da takalma ko kuma waɗanda nasu s**a lalace. Wasu daga cikinsu na rayuwa ne cikin mawuyacin hali, ba tare da ikon sayen sabbin takalma ba.
Domin rage musu radadi, Haske Support Foundation ta raba takalma ga mabukata, domin sauƙaƙa musu wahalhalu tare da taimakawa wajen kare lafiyar ƙafafunsu.
A ƙarshe, muna gode wa Allah (SWT) da Ya ba mu damar gudanar da wannan aiki na alheri. Muna roƙonSa da Ya ƙara mana ikon ci gaba da taimakon al’umma, Ya kuma wadata ƙasarmu da zaman lafiya, ci gaba, da haɗin kai mai ɗorewa.
Signed:
Haske Support Foundation
20th April, 2026
Jawabin Shugaban The Ward Head Unity Forum of Jos North LGA, A Yayin Bayar da Lambar Yabo ga Hajiya Maryam Shehu Nabage (Uwar Marayu)
Hakika, wannan karramawa ba wai kawai alama ce ta yabo ba, shaida ce ta irin gagarumin aikin alkhairi da ta dade tana yi ba tare da gajiyawa ba. Ta hanyar gidauniyarta, Haske Support Foundation, ta taimakawa marayu, zawarawa, masu nakasa da sauran mabukata a cikin al’umma, ta yadda Al'umma da dama s**a samu sauyi mai ma’ana.
Uwar Marayu ta zama abin koyi na tausayi, juriya da sadaukarwa. Duk wanda ya san ta ya san cewa ko da tana cikin nata ƙalubalen, ba ta taɓa daina miƙa hannu ga masu buƙata ba. Wannan hali nata ya sa ta zama ginshiƙi a cikin al’umma, kuma abin alfahari ga Jos North da ma Najeriya baki ɗaya.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara mata lafiya, Ya ba ta ikon ci gaba da wannan aiki mai albarka, Ya saka mata da aljannatul Firdausi.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Contact the organization
Telephone
Address
Tudun O. C. Rikkos, Jos North
Jos