Mairakumi
01/10/2025
Sheikh Bala Lau Ya Yi Kira da A Sasanta Rikicin Kano Cikin Lumana, Ya Yabi DSS Kan Rawar da Ta Taka
Shugaban Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta tarayyar Nigeria, Ash-Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau , ya yi kira da a kwantar da hankali da nuna haƙuri wajen tafiyar da rikicin addini da ke ci gaba a Kano, inda ya gargadi mutane da su guji amfani da lamarin don haifar da rarrabuwar kawuna a cikin al’ummar Musulmi.
A lokacin da yake gabatar da wa’azi a makon jiya wajen taron ƙungiyar ‘Federation of Ahlusunnah Organization in Nigeria’ (FAFSON) da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo, Sheikh Bala Lau ya yaba da hangen nesa da kwarewar Darakta Janar na Hukumar Tsaro na Farin kaya (DSS), Mista Tosin Ajayi, wajen tabbatar da lamarin zuwa hanyar zaman lafiya ba tare da zuwa kotu ba.
“Ina yabawa shugabancin DSS bisa tabbatar da cewa an tafiyar da wannan al’amari cikin hikima da lumana. Kai shi kotu zai iya tada jijiyoyin wuya kuma ya tsawaita rikicin. Abin da al’ummar Musulmi ke buƙata a yanzu shi ne hikima, haƙuri da haɗin kai,” in ji shi.
Malam ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta ci gaba da zama tsaka-tsaki, yana jaddada cewa shiga gefen kowane ɓangare na iya ƙara rarrabuwar kai da lalata zaman lafiya a jihar.
“A irin wannan lokaci, bai kamata gwamnati ta nuna tana goyon bayan ɓangare guda ba. Adalci da gaskiya suna buƙatar a tsaya a tsaka-tsaki. Aikinmu a matsayin shugabanni shi ne kiyaye zaman lafiya, ba ƙara wa rikici wuta ba,” in ji Sheikh Bala Lau.
Jawabansa sun biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da aka gabatar tare da mayar da martani ga Majalisar Shura ta Jihar Kano kan zargin kalaman batanci da ake alakanta Shi da Sheikh Lawan Shuaibu Abubakar Triumph. Majalisar ta bayyana cewa za ta saurari masu ƙorafi da kuma malamin kafin ta ba da wani shawari ga gwamnati.
Sai dai Sheikh Bala Lau ya yi kira ga Musulmi da kada su bari zarge-zargen su rinjaye su, yana gargadi cewa irin waɗannan muhawarori idan ba a kula ba za su iya bata sunaye kuma su kau
29/09/2025
Idan Zà A Kàshè 'Yañ Sandà Dari A Matsayin Hukuncin Kashe Danà Da Aka Yì, Bai Zai Yì Daidai Da Ran Dan Nawa Ba, Domin Ni Ďànà Hafizin Kùr'anì Nè, Cewar Mahaifin Salim, Wanda Ya Mutu A Komar 'Yañ Sanda A Kano
Mahaifin nasa ya cigaba da cewa zai cigaba da bibiyar binciken da ake yi koda komai nasa zai kare ne, saboda an cutar da su.
28/09/2025
Gwamnatin Tarayya Ta Karyata Ikirarin Kisan Kare-dangi Kan Kiristoci a Najeriya.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ba gaskiya ba ne kuma yaudara ce rahotannin da wasu kafafen ƙasashen waje ke yadawa cewa ana kisan kare-dangi na addini ga Kiristoci a ƙasar.
Gwamnatin ta ce waɗannan ikirari na ƙarya ne kuma suna nufin bata sunan Najeriya a idon duniya. Ta kuma bayyana cewa Najeriya ƙasa ce mai yawan al’umma daban-daban da addinai daban-daban waɗanda ke zaune tare cikin lumana, tare da samun kariya ta doka ga kowa ba tare da nuna bambancin addini ba.
Haka kuma gwamnatin ta yi kira ga ‘yan ƙasa da su guji yarda da irin waɗannan rahotanni marasa tushe kuma su ci gaba da zaman lafiya da juna domin ci gaban ƙasa.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Hadejia