Koya Gida
Allah ya gafartawa iyayanmu
اللهم أغفر لنا والإخوان الذين سبقون بإيمان
ME YA SA ADDININ MUSLUNCI YA TSOLE MA TURAWA IDO?
Wata rana mun yi rubutu, a ciki sai muka yi ishara cewa; Muslunci shi ne Addinin da Turawa suke yaka. To sai wani daga cikin yaran Turawan masu izgilanci ga Addinin Muslunci yake cewa; ta yaya Turawa za su tsaya su bata lokacinsu wajen yakar Addinin jahilci da cibaya?!
To abu ne sananne cewa; Yaki da yake gudana a yau yaki ne a kan Madogaran tsarin rayuwa. Yaki ne tsakanin tsarin rayuwa da ya ginu a kan Addini, da kuma tsarin rayuwa da ya ginu a kan watsi da Addini (secularism & modernism).
Ita madogarar tsarin rayuwa ta Addini, Addinin Kiristanci da Addinin Yahudanci sun fadi warwas a gaban tsarin rayuwa bisa madogara ta watsi da Addini (secularism & modernism). Ma'ana; Addinin Kiristanci da Yahudanci duka sun gaza wajen tunkarar tsarin watsi da Addini (secularism & modernism), saboda Addinai ne da aka lalata su aka gurbata su, aka gurbata littatafan da aka saukar musu.
Shi dai Yahudanci da ma Addini ne na gado da kabilanci ba Addini ne na kiran mutane su shiga cikinsa ba, mutum ba zai zama Bayahude ba sai in iyayensa Yahudawa ne, musamman uwarsa mahaifiya. Don haka Addini ne na kabilanci. Wannan ma yana daga cikin dalilai da s**a sa Yahudancin ya kasa tunkaran tsarin rayuwar watsi da Addini (secularism & modernism).
Amma shi kuma Kiristanci tun tuni ya fadi a gaban madogarar watsi da Addini (secularism & modernism), tun lokacin da aka gurbata shi aka shigar da almara masu yawa cikinsa. Babbar almarar da s**a kirkira ita ce cewa; Allah uku ne Allah daya. Da almaran cewa; Allah ya shiga jikin Annabi Isa (as). Har kuma lokacin da aka shata fagen yaki tsakanin Malaman Coci da Malaman Kimiyya da Fasaha, inda Coci ya yaki duk wani binciken Kimiyya da aka yi aka gano Nazariyya da abubuwa na hakika da s**a saba ma karantarwan Coci da Bible.
To a nan ma dai Kiristanci ya gaza a wannan dagar da s**a yi da Malaman Kimiyya, wannan ya sa aka yi watsi da Kiristanci a Turai, a koma tsarin rayuwa bisa madogarar watsi da Addi
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Koya Kano Nigeria
Gwarzo