GOMBE PDP DAILY Reporters

GOMBE PDP DAILY Reporters

Share

28/02/2026

Baya ta haihu: APC ta sauya tsarin rabon shugabancin jam'iyya a Kano zuwa 50–50 maimakon 60-40

Uwar jam’iyyar APC ta ƙasa ta sauya tsarin rabon iko a jihar Kano daga kaso 60–40 da ta amince da shi a farko zuwa 50–50 tsakanin bangaren Gwamna Abba Kabir Yusuf da bangaren tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin.

Sauyin ya biyo bayan taron karɓar Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, zuwa APC a ranar 16 ga Fabrairu, wanda ya gudana a Kano

Jaridai Daily Nigerian ta rawaito cewa taron ya bar baya da Kura, inda jam'iyyar ta lura cewa, shugabannin APC na asali ne s**a tara jama'a a taron ba wai Gwamnan Kano ba, hakan ne yasa ta ce da sake, wai an bai wa mai kaza kai, in da ta sake ragewa gwamna Abba kaso 10 a cikin sittin din shi, ta kara wa bangaren Ganduje da Barau.

Sabon tsarin ya tanadi rabon 50–50 tsakanin bangarorin biyu, a wani yunƙuri na tabbatar da daidaito da kuma rage rikicin cikin gida. Rahotanni sun ce shugabannin jam’iyyar a matakin ƙasa sun nuna rashin gamsuwa da yadda taron sauyin sheƙar bai jawo dimbin magoya bayan Kwankwasiyya ba kamar yadda ake zato.

Duk da sauyin sheƙar wasu ‘yan majalisa, kwamishinoni da shugabannin ƙananan hukumomi 44, ana ganin tushen magoya bayan Kwankwasiyya na nan daram tare da jagoranta, Rabiu Musa Kwankwaso.

A wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano, an cimma daidaito inda aka bai wa gwamnan kujeru 14 cikin 27 na shugabannin ƙananan hukumomi, yayin da bangaren Ganduje ya samu 13.

Majiyoyi sun tabbatar wa da jaridar cewa matakin ya samu amincewar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, domin tabbatar da daidaito da ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar a Kano.

Masu sa ido na ganin sabon tsarin na 50–50 na iya rage zazzafan rikicin cikin gida, sai dai ana jiran a gani ko zaman lafiyar bangarorin biyu zai dore ko kuma sabbin rikice-rikice za su ɓulla a nan gaba.
GOMBE PDP DAILY Reporters
PDP GOMBE STATE

28/02/2026

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar PDP da s**a bar jam’iyyar zuwa wasu bangarori da su sake yin nazari tare da dawowa PDP, yana mai cewa abubuwan da s**a faru na zaben kananan hukumomin babban birnin tarayya Abuja sun zama manuniya cewa jam'iyyar hadaka ta ADC bata da tasiri.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron shan ruwan azumin watan Ramadana da aka shirya wa masu ruwa da tsaki daga shiyyar Bauchi ta Kudu da Bauchi ta Tsakiya.

A cewarsa, wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar sun bar PDP ne da zaton za su samu tasiri a wani wuri, amma Allah Ya nuna musu akasin hakan.

“A cikinmu akwai waɗanda suke tsammanin za su je wani waje su yi wani tasiri, Allah ya nuna musu babu tasiri a wajen, duk ƙarfinsu, duk girmansu, duk kimarsu, Allah ya ƙaskantar da su,” in ji gwamnan.

Ya ce wannan ya zama darasi da ya kamata ya sa su tsaya su yi tunani mai zurfi kan matakin da s**a dauka.

“To wannan manuniya ce, ya kamata su yi la’akari, su yi kiyamullaili wa kansu, wannan jam’iyya ta PDP da ta yi musu komai su dawo cikinta,” ya kara da cewa.

Gwamna Bala Mohammed ya jaddada cewa bai dace mutum ya bar inda yake da karfi da nasara saboda dalilin mutum guda ba.

“Ba za ku tashi ku bar wajen da kuke da ƙarfi ba, wajen da kuka ci zaɓe, kuka yi shugabanci a ƙasa, kuka yi shugabanci a wasu jihohi ku tafi wani waje saboda mutum ɗaya ba. Wannan sakarci ne,” ya bayyana.

“Daga an taɓa su su ce Wike. To waye Wike? Mutum ɗaya ya kore ku, ai bai kamata ba ko. Shima Wike yana siyasarsa ne na yadda zai tsira da kansa, to mu ma sai mu yi siyasarmu na yadda za mu tsira da kanmu,” in ji shi.

@

07/08/2025

Alhamdulillah!

Goodluck Jonathan Has accepted to run against Tinubu in 2027🥱 Jonathan Ya Amince Zaiyiwa PDP Takara.💪

Want your business to be the top-listed Media Company in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Pantami
Gombe