Mus'abmk

Mus'abmk

Share

Photos 24/01/2017

Allah Yaja Kwana Baba

Photos 01/01/2017

Yadda zamu inganta Nigeria a 2017 -inji Buhari

A sakonsa ga al'ummar Nijeriya na sabuwar shekarar 2017, Shugaba Muhammad Buhari ya sake jinjinawa sojojin Nigeria bisa kwato dajin Sambisa.

Buhari wanda ya kalubalanci 'Yan Shi'a da kungiyoyin tsageru kan Zaman Lafiya, ya nemi su shiga taitayinsu.

Ko da yake dai mista Buhari ya nemi kungiyar Shi'ar da tsagerun Niger Delta kan su rungumi zaman lafiya tare da bin dokokin kasar a yayin da aka shiga sabuwar shekara amma yace ba za'a lamunci tsageranci ba.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bin hanyoyin yin sulhu da wadannan kungiyoyin inda ya sake rokon mayakan Niger Delta kan su daina fasa bututun mai, su zo a zauna kan teburin zaman lafiya. Sannan sai ya nemi jami'an tsaro su rika mutunta wadannan kungiyoyi a duk lokacin da wata rigima ta hada su.

Haka nan kuma Shugaba Buhari ya jaddada cewa dole 'yan Nigeria su zauna da junansu cikin mutunci da girmamawa yana mai cewa wadannan rukunai biyu ne kadai za su tabbatar da ci gaba da zaman kasar a matsayin dunkulalliyar kasa mai yanci.

Shugaban kasar ya kuma tabbatar da kurakruran da gwamnatinsa ta yi wajen kula da 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya rutsa da su inda ya ce za'a gyra a sabuwar shekara.

Ya ce nasarar da aka samu wajen fatattakar mayakan Boko Haram daga hedkwatarsu da ke cikin Dajin Sambisa ya bude sabon faifai a tarihin tsaron lafiya a Nigeria inda ya nemi 'yan Nijeriya kan su sanya ido kan bakin fuska da s**a gani a cikinsu tare da kai rahoto kan duk wani abu da basu gamsu dashi ba ga jami'an tsaro.

Buhari ya kuma bayyana cewa shirinsa na ganin Nigeria na ciyar da kanta, ya fara tasiri musamman yadda a wannan shekarar manoma s**a sami amfanin Gona mai yawan gaske sannan kuma wasu jihohi sun shiga cikin wasu yarjejeniyoyi da bankuna don samar wa manoman jihohinsu rancen noma mai saukin biya.

A karshe, Shugaba Buhari ya sha alwashin kyautata jin dadin yan Nigeria domin cin gajiyar cenjin da s**a zaba. Sannan ya kara da taya Al'ummar Nigeria fatan Alheri na shiga sabuwar shekara ta 2017.

Allah Ya Taimaki Shugaba Muhammadu Buhari
Allah Ya Taimaki Al,ummar Najeriya
Allah Ya Bamu Zaman Lafiya A Kasarmu Najeriya.......Ameen

Photos from Mus'abmk's post 31/12/2016

An Mika Wa Buhari Tutar Shekau Da Al-Qur'ani Da Aka Gano A Dajin Sambisa

Shugaban rundunar Soja na 'Zaman Lafiya Dole', Manjo Janar Lurky Irabor ya mika wa Shugaba Muhammad Buhari ainihin Al-Qurani da tutar da Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ke amfani da su wadda aka gano a Dajin Sambisa bayan fatattakan mayakan kungiyar da sojoji s**a yi.

Sai dai, a yayin karbar tutar wanda aka gudanar a wurin liyafar da rundunar tsaron Fadar Shugaban kasa ta shirya a Abuja, Shugaba Buhari bai ce Uffan ba game da ikirarin Shekau na cewa har yanzu kungiyar na da tasiri a dajin Sambisa.

Want your establishment to be the top-listed Bar/pub in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Gombe