AMT News

AMT News

Share

24/06/2026

Jam’iyyar PDP ta bai wa Farfesa Isa Ali Pantami takardar shaidar zama ɗan takarar gwamnan Gombe

Jam’iyyar PDP ta ƙasa ta bai wa Professor Isa Ali Pantami takardar shaidar zama halastaccen ɗan takararta na gwamnan jihar Gombe a zaɓen shekarar 2027.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani saƙo da Abba Sani Pantami, ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce an miƙa takardar shaidar ne yayin wani taron jam’iyyar da aka gudanar a Abuja.

A cewar saƙon, PDP ta gudanar da taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) tare da rantsar da sabbin shugabanninta na wa’adin 2026 zuwa 2030.

Saƙon ya ƙara da cewa jam’iyyar ta kuma bai wa sauran ‘yan takararta na gwamna takardun shaidar zama halastattun ‘yan takara bayan an sanya sunayensu cikin jerin ‘yan takarar da aka ce za su wakilci jam’iyyar a zaɓen 2027.

27/05/2026

Yayin da Pantami ke zayyano wasu tarin nasarori da PDP tayi a Gombe

26/05/2026

Yayin da magoya baya ke taya Pantami murnar samun takarar gwamna a jam'iyar PDP a Gombe

Facebook BBC Hausa RFI Hausa

Want your business to be the top-listed Media Company in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Gombe