Madubi - H

Madubi - H

Share

09/07/2026

Da Naira 300 kacal zaku samu 1GB na Data mai kyau a Manhajar ABBA PANTAMI DATA.

Kuyi Download din Manhajar ABBA PANTAMI DATA ta wannan link din a PlayStore da kuma AppStore
👇👇
Ga link din PlayStore
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.com.abbapantamidata.app

Ga link din AppStore
https://apps.apple.com/us/app/abba-pantami-data-ltd/id6744061271

Mai bukatan karin bayani, ya tuntubi daya daga cikin customer care ta WhatsApp.

09138275183
08126081967
07046868000
08104049265

Photos from Madubi - H's post 08/07/2026

'Gani Ya Kori Ji': Aikin titin Zariya–Funtuwa–Gusau–Sakkwato zai ƙarfafa tattalin arzikin Arewa

Tawagar manema labarai da ke rangadi a ƙarƙashin shirin "Gani Ya Kori Ji", tare da Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ta kai ziyara sashe na farko na aikin titin Zariya–Funtuwa–Gusau–Sakkwato, wato ɓangaren Zariya–Funtuwa–Sheme, domin duba yadda aikin ke gudana da kuma tantance irin ci gaban da aka samu.

A yayin ziyarar, jami'an da ke kula da aikin sun bayyana cewa titin na daga cikin manyan ayyukan more rayuwa da Gwamnatin Tarayya ta bai wa fifiko saboda muhimmancinsa wajen bunƙasa tattalin arziki da sauƙaƙa zirga-zirga a Arewacin Najeriya.

Sun ce duk da cewa an amince da fara aikin tun a gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta faɗaɗa aikin ta hanyar mayar da shi daga hanya mai layi ɗaya zuwa babbar hanya mai layuka biyu (Dual Carriageway), domin dacewa da ƙaruwa da yawan ababen hawa da kuma buƙatun ci gaban yankin.

A cewarsu, idan aka kammala aikin, titin zai haɗa jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara da Sakkwato cikin sauƙi, tare da inganta zirga-zirgar matafiya da jigilar kayan amfanin gona, dabbobi da sauran kayayyakin kasuwanci.

Jami'an sun ƙara da cewa aikin ya haɗa da sake gina titin baki ɗaya, gina sabbin gadoji, magudanan ruwa, ƙarin layukan mota da kuma samar da kayayyakin tsaro na zamani, waɗanda ake sa ran za su rage haɗurran hanya tare da inganta lafiyar matafiya.

Sun kuma bayyana cewa tun kafin a kammala aikin, ya riga ya samar da dubban guraben ayyukan yi ga injiniyoyi, masu sana'o'in hannu, direbobin injuna da sauran ma'aikata. Ana kuma sa ran idan aka gama shi, zai rage kuɗin sufuri, ƙara bunƙasa kasuwanci, jawo masu zuba jari da kuma ƙarfafa alaƙar tattalin arziki tsakanin jihohin Arewa maso Yamma da sauran sassan ƙasar.

Manema labaran da ke cikin shirin "Gani Ya Kori Ji" sun ce rangadin ya ba su damar gani da ido kan yadda manyan ayyukan gwamnatin tarayya ke gudana. Sun bayyana aikin titin Zariya–Funtuwa–Gusau–Sakkwato a matsayin wani muhimmin aikin raya ƙasa da ke nuna ƙudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta ababen more rayuwa, bunƙasa tattalin arziki da kuma inganta rayuwar al'ummar Najeriya ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata.

08/07/2026

Mansura Isah Ta Sake Komawa Kungiyar Triple R na Rarara Bayan Ficewarta

Jarumar Kannywood, Mansura Isah, ta sake komawa ƙungiyar Triple R bayan ficewar ta daga cikin kungiyar.

An dai hangi ta tare da sauran mambobin ƙungiyar a wani hoto da ke yawo a shafukan sada zumunta.

A baya dai, ficewar Mansura daga Triple R ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin mabiyan ta a shafukan sadarwa, inda mutane da dama s**a riƙa bayyana ra'ayoyi da hasashe kan abin da ya haddasa matakin da ta ɗauka.

Sai dai zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga Mansura Isah ko shugabannin ƙungiyar Triple R da ke bayyana dalilin komawarta ko kuma abin da ya sa ta fice tun farko.

Want your business to be the top-listed Media Company in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Gombe