Jewel Multimedia

Jewel Multimedia

Share

Photos from Jewel Multimedia's post 02/12/2025

SRC Ta Raba Tallafi a Masaukan Daliban Jami’ar Tarayya Kashere

Majalisar Wakilan Dalibai ta Jami’ar Tarayya Kashere (SRC) ta gudanar da rabon tallafi ga daliban mazauna masaukan jami’ar, a wani mataki da aka bayyana a matsayin ci gaba wajen inganta walwalar ɗalibai da kyautata yanayin rayuwarsu. An gudanar da wannan aiki ne a ranar Litinin, 1 ga Disamba 2025.

A yayin bikin rabon kayan, Shugaban SRC, Kwamared Kabir Faizu Danyaya, ya ce wannan shiri na daga cikin ƙudurin majalisar na ganin cewa ɗalibai sun samu dukkan irin tallafi da kulawa da ya dace. Ya bayyana cewa SRC na ɗaukar walwalar ɗalibai a matsayin abin da ya fi komai muhimmanci a aikinsu na yau da kullum. Danyaya ya jaddada cewa taken su na “Ba a Bar Kowa a Baya” ya kasance mabudin ƙarfafa majalisar wajen ɗaukar matakai masu tasiri ga dalibai.

Shugaban sashen kwanan Dalibai, Dahiru Sulaiman Gwale, wanda ya karɓi kayan a madadin daliban masaukan, ya bayyana tallafin a matsayin wani abu da ya zo a daidai lokacin da ake buƙatarsa. Ya ce tsananin buƙatar kayayyakin tsafta da sauran kayan amfani na yau da kullum ya sa wannan tallafin ya zama abin jin daɗi ga dalibai, musamman duba da ƙalubalen da ake fuskanta a masaukan.

Wasu daga cikin daliban da s**a samu tallafin sun bayyana farin cikinsu tare da jinjinawa majalisar bisa ga jajircewarta. Sun ce matakin na nuna cewa majalisar na bibiyar kalubalen da dalibai ke fuskanta tare da ɗaukar matakai kai tsaye ba tare da jinkiri ba.

Kayan da aka raba sun haɗa da robar ruwa, mujajjawa (moppers), tsintsiya, sabulai, Hypo da sauran muhimman kayan tsaftace muhalli kayan da ake amfani da su akai-akai wajen tabbatar da tsafta da ingantaccen yanayi a masaukan jami’ar.

Wannan shiri dai ya ƙara ƙarfafa gwiwar daliban cewa akwai ci gaba a aikace a tsakanin shugabannin majalisar, musamman wajen kula da buƙatun ɗalibai da kuma kawo sauƙi a rayuwar su.

Photos from Jewel Multimedia's post 24/10/2025

Sheikh Professor Isa Ali Pantami Ya Sa An Rushe Masallacin Kofar Hakimin Pantami, Zai Gina Sabon Masallaci Na Zamani

Babban malamin addinin Musulunci kuma tsohon Ministan Sadarwa na Najeriya, Sheikh Professor Isa Ali Ibrahim Pantami, CON (Majidadin Daular Usmaniyya), ya bayar da umarnin rushe tsohon Masallacin Kofar Hakimin Pantami da ke cikin garin Gombe, domin gina sabon masallacin Juma’a na zamani a wurin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, bayan rushewar masallacin, Sheikh Pantami ya sayi gidaje uku da ke gefen masallacin, domin fadada fili da samar da isasshen wurin ibada ga jama’ar da ke halartar sallar Juma’a.

A cewar mazauna yankin, wannan aiki na Sheikh Pantami ya zama abin yabo, ganin yadda tsohon masallacin ke da ƙaramin fili da kuma cunkoso, musamman a lokutan sallar Juma’a.

Wani daga cikin mazauna unguwar, Malam Abdullahi Haruna, ya bayyana cewa wannan mataki ya nuna irin kishin da Sheikh Pantami ke da shi ga addini da al’umma.

Sheikh Pantami mutum ne da ke nuna kishin addini da kulawa da jama’a. Wannan aiki da yake yi zai taimaka wajen kawo sauƙi da kwanciyar hankali ga masu ibada. Allah ya saka masa da alkhairi,” in ji shi.

Ana sa ran sabon masallacin da za a gina zai kasance na zamani, mai ɗauke da kayayyakin more rayuwa da tsarin da ya dace da zamani ciki har da na’urorin sanyaya iska, tsarin sauti na zamani.

Wannan aikin na cikin jerin ayyukan alkhairi da Sheikh Pantami ke gudanarwa a fadin ƙasar nan, musamman waɗanda s**a shafi gina masallatai, tallafawa malamai, da taimakon al’umma ta fannoni daban-daban.

A ƙarshe, jama’ar yankin sun roƙi Allah Ya saka wa Sheikh Pantami da alkhairi, tare da jinƙan iyayensa.

Want your business to be the top-listed Media Company in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Gombe
1238