Hantsi Post
26/08/2023
WANNAN SHINE MATASHI ABDULBAKI JARI WANDA YA KIRKIRO A DUNIYA
Abdulbaki Jari, shine wanda ya ƙirƙiro wannan rana ta Hausa a Duniya baki ɗaya a shekarar 2015, ma'aikacin sashin Hausa na gidan rediyon BBC Hausa ne, ya kasance ƙwararre kuma haziƙin ɗan jarida da gidan rediyon take alfahari da shi.
A yau ƙasashe sama da goma ke alamta wannan rana domin bayyana daraja da kuma martabar Yaren Hausa a Duniya.
Bayan wannan ƙoƙari, ya ƙara da ƙoƙarin samar da rubutun da Hausawa zasu dogara da shi kamar ko wani Yare a Duniya, amma hakan bai samu ba.
Ina ƙira ga Hausawa na ciki da wajen Najeriya da su kasance wakilan Hausawa na gaskiya, ku daina amfani da wannan rana wajen yaɗa abun da sam bai dace da Yaren Hausa da Hausawa ba.
Daga ƙarshe ina muku addu'a da fatan Allah ya ƙara ɗaga darajar wannan Yare da nima ya zama yaren da nafi mu'amala da shi a Duniya duk da ba nawa bane.
Rubutawa: Mustapha Abubakar Kwaro
26/09/2023
27/03/2023
DA ƊUMI ƊUMIN SA - Mawaƙan Hausa Rarara & Baban Cinedu, sun bayyanar da Cewar ɓarnar da akayi masu a lokacin murnar sabon gomnan jahar kano, sun tabbatar da cewar babu wanda yabasu komai akan su rage hasara! (Rara& Baban Cinedu )
Daga Suleiman Umar Faruk
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Ganye