Formula 9 formula 8
17/01/2026
🧿 ADDINAN ALJANU DA IRE-IREN SU
📘 BABI NA HUƊU
LIILAJI WALMASI SHAIDAN.
🧿 Addinan Aljanu da Ire-irensu
🕌 Ka sani, ya kai ɗan’uwa Musulmi, cewa aljanu suna da addinai mabanbanta, kamar yadda mutane ma suke da addinai daban-daban.
👉 A cikinsu akwai:
❌ Kafirai gaba ɗaya
✡️ Yahudawa
✝️ Kiristoci (Nasara)
☪️ Musulmi, daga cikinsu:
😔 Musulmi masu fasikanci
🌟 Musulmi masu tsoron Allah (muttaqiun)
🤝 Akwai Sahabbai daga cikin Aljanu
📜 A cikin aljanu, akwai sahabbai, kamar yadda aka samu sahabbai daga cikin mutane.
Wannan abu sananne ne ga malamai, kuma akwai ijma’i (yarjejeniya) a kansa.
📚 Imam Ibn Hajar (رحمه الله) ya ambaci haka a cikin littafinsa Al-Isābah fī Tamyīz aṣ-Ṣaḥābah cewa akwai wani babi da ya keɓe sahabban aljanu daga cikin sahabban Annabi ﷺ.
📖 Hujja daga Al-Kur’ani
Allah Maɗaukakin Sarki Ya faɗa mana a Suratul Jinn cewa aljanu suna cewa:
“Bayan haka Kuma a cikinmu akwai masu adalci, kuma a cikinmu akwai waɗanda ba haka ba; mun kasance da hanyoyi mabanbanta.”
📍 (Suratul Jinn: 11)
🌍 Aljanu Ƙungiyoyi ne Masu Bambanci
🧠 Malamai sun ce:
Aljanu ƙungiyoyi ne daban-daban, kuma suna da addinai mabanbanta.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya fadi haka kuma a cikin surar nan:
“Hakika Kuma lalle mu, lokacin da muka ji shiriya, mun yi imani da ita.
Duk wanda ya yi imani da Ubangijinsa, ba zai ji tsoron cutarwa ko zalunci ba.”
“Kuma a cikinmu akwai Musulmi, kuma a cikinmu akwai azzalumai.
To, wandanda s**a musulunta, su ne masu neman shiriyar Allah.
“Amma azzalumai kuwa, daga cikin mu sun zama itacen wutar Jahannama.”
📍 (Suratul Jinn: 13–15)
Domin bukatar ƙarin bayani ko shawara ko maganin akan dukkan nau'i shafar aljanu ko sihir ko kammun baka ko akan wasu matsalolin daban daban zaku Iya tuntubar mu 08152753609/08029665783
14/01/2026
👳♂️ LABARIN WANI SAHABIN ANNABI ﷺ DA BARAWO.
An kuma ruwaito wata kissa cewa:
Wani mutum daga cikin Sahabban Annabi ﷺ yana da shago da aka rufe, yana kasuwanci da dukiyarsa.
Wata rana ya fita kamar yadda ya saba, sai barawo ya tare shi.
Barawon ya ce masa:
“Ka ajiye abin da ke tare da kai, in ba haka ba zan kashe ka.”
🤲 Bukatar Sahabin Kafin Mutuwa
Sai Sahabin ya ce masa:
“Ba na so komai sai abu ɗaya kacal:
*Barawon yace masa wanne abune kake bukatar?*
Sai wannan sahabin yace masa:
👉 ka bar ni in yi sallah raka’a biyu.”
Daganan wannan Barawon ya amince.
🕊️ Addu’ar da Ta Sauko masa Daga Sama🏰🤚🖐️
Bayan ya yi sallah, a sujada ta ƙarshe, sai Sahabin ya yi wannan addu’a:
“Ya Wadūd, Ya Wadūd, Ya Maɗaukakin Al’arshi,
Ya Mai aikata abin da Ya so,
Ina roƙonKa da girman mulkinka da ba ya gushewa,
da hasken fuskarka da ya cika sammai da ƙasa,
Ka kare ni daga sharrin wannan barawon.”
⚔️ Allah madaukakin ya Amsa Addu’a nan a Take🤲
Da barawon ya ɗago kansa, sai ya ga wani jarumi a kan doki, da takobi a hannunsa.
Sai jarumin ya bugi barawon, ya kashe shi.
Sai Sahabin ya tambaye shi:
“Wane ne kai?”
Sai ya ce:
🕊️ “Ni mala’ika ne daga sama ta huɗu.
Da ka yi addu’ar ka, sai Allah yaji kiranKa, Daga nan Allah madaukakin sarki Ya aiko ni.”
📜 Maganar Anas bn Malik (رضي الله عنه)
Anas bn Malik (Allah Ya yarda da shi) ya ce:
“Duk wanda ya yi wannan addu’a bayan alwala,
ya yi sallah raka’a huɗu,
to Allah zai amsa masa addu’arsa,
ko da ta shafi abin da aka riga aka ƙaddara shine.
Allah ne mafi sani.”
🕊️ Kammalawa
✨ Wannan labari yana nuna:
Girman addu’a
Karfin komawa ga Allah alokacin da aka shiga acikin tsanani,da kuma ƙunci.
Cewa Allah Yana amsa addu’ar mai tsananin buƙata
Kuma Yana turo taimako daga inda ba a zata ba
🤲 Allah Ya sa mu kasance daga cikin masu yawan addu’a da samun amsa warta da karɓar ta nan take. Ameen.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Jani House Funtua Jihar Katsina
Funtua
2030