YouKay Media Stream

YouKay Media Stream

Share

05/12/2025

Alh. Ahmad Muhammad Sani CON @45 .
Allah ya karawa Sarki lafia ...

28/11/2025

A wani rahoton da Sahara Reporters ta fitar, ya nuna cewa gwamnatin Jihar Jigawa ta ware Naira miliyan 800m domin gina da kuma kayayyata masaukin shugaban kasa (Presidential Wing) a fadar Gwamnatin Jiha, da kuma Naira miliyan 50m don gina sabon wajen wanki da guga (laundry facility) na Gwamna.

Binciken ya kuma gano cewa tsakanin Janairu zuwa Satumbar 2025, an kashe Naira miliyan 672 wajen siyan motocin gidan gwamnati, ciki har da Naira miliyan 437 da aka kashe cikin watanni uku kacal (Yuli–Satumba).

Rahoton ya kuma ce an samu sabbin motocin alfarma a fadar gwamnati, duk da cewa gwamnati ta musanta cewa an sayi sabbin motoci, tana cewa Gwamna Namadi har yanzu yana amfani da tsoffin motocin da ya gada.

Jam’iyyar APC ta bayyana rahoton a matsayin jita-jita ne, yayin da wasu majiyoyi ke zargin cewa kudaden siyan motocin sun yi yawa fiye da kima kuma an yi amfani da gurbatacciyar hanya wajen gudanar da kwangilolin.

Har yanzu ba a sani ba ko nawa za a ƙara kashewa kan motocin gidan gwamnati kafin ƙarshen shekarar 2025.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Dutse?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address


Yalwawa Quaters Bypass Dutse
Dutse
0234