Ibrahim Salihu
Ramadan
04/05/2025
اللهُـمِّ اغْفِـرْ لِـ-فُلاَنٍ (باسـمه)وَارْفَعْ دَرَجَتََـهُ فِي المَهْـدِيّيـنَ ، وَاخْـلُفْـهُ في عَقِـبِهِ في الغَابِِـرِينَ، وَاغْفِـرْ لَنَا وَلَـهُ يا رَبَّ العـالَمـين، وَافْسَـحْ لَهُ في قَبْـرِهِ وَنَـوِّرْ لَهُ فِيهِ
Sanarwa Daga CUPS!
Jama'a barkanmu da warhaka. Ina murnan sanardaku cewa muna ci gaba da gwada technology wadanda zamuyi amfani da su wajen horaswa na CUPS Computer and ICT Training. Munyi gwaji ranan Asabar da jiya Lahdi. Kome na tafiya yadda muka tsara. Alhamdulillah.
Kamar yadda kuka sani, a yanzu haka munyi ragista na mutane dubu goma sha shida (16,000). Mun rufe kafan yin ragista sai mun kammala training wadannan tukuna. Muna da kudurin training matasanmu da zawaranmu da marayummu su dubu dari (100,000) a zagaye na farko. Amma babban burinmu shine muyi training mutane million daya (1,000,000). Allah Ubangiji Ka daafa mana. Amin.
Insha Allah, zamu fara training da karfe 4.30 PM, ranan Lahdi, 2/3/2025. Zaku sami email na gayyata daga Malami wadda zaiyi mukuma horaswan. Zamu sa bayanai da yawa a dandalinmu na Telegram. Ku dubi sashin comments domin samun link din.
Wajen bada darasi, zamuyi amfani da wani software mai suna Microsoft Teams. Ku dubi sashin comments domin samun link din Microsoft Teams. Kuyi kokari kuyi downloading wannan software din a salulanku ko computer.
Jama'a ku taimakemu da addu'a da fatan Alheri. Allah Ubangiji Ya bamu gagarumar nasara akan wannan tafiya na ceton Arewa da al'ummanta. Amin Ya Rabbi.
Jama'a na barku lafiya.
Dr. Idris Ahmed.
CUPS.
24/2/2025.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Biu