Excellency DailyTrust
10/03/2026
YAƘIN IRAN.....
Al'amura na neman rincaɓewa bayan da NATO ta fara fusata.....
Ga halin da aka wuni zuwa yammacin yau.....
IRAN
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yace Tehran tayi matuƙar shiryawa yaƙi saboda haka babu gudu babu ja da baya, a dai dai lokacin da yaƙi yake shiga kwana na 9 ( Al'Arabiyya English )
UAE
Ministan tsaron hadaddiyar daular Larabawa yace ƙasar ta kakkaɓo mizayil 12 da jirgi maras matuƙi 17 a sararin samaniyar kasar a hare haren da Iran ta kaddamar. ( Al'Arabiyya English )
TURAI
Tarayyar Turai tace babu wani ƙaramcin man fetur da nahiyar ke fuskanta a sakamakon yaƙin dake gudana a gabas ta tsakiya ( EU )
RASHA
Putin yace zasu baiwa sabon shugaban addinin Iran Mojtaba khamene'i gudunmawar data dace iya karfin su ( Vladimir Putin )
KUWAIT
Rundunar sojin saman Iran ta kaddamar da harin jirgi maras matuƙi a wani ɓoyayyen sansanon sojin Amurka a Kuwait a ranar Litinin ɗinnan. ( Irna News Agency )
GERMANY
Wani cansala a Jamus Friedrich Merz yace Iran ce cibiyar ta'addanci ta Duniya, kuma ya zama dole a shafe tarihin ta matukar Duniya tana neman zaman lafiya. ( Friedrich Merz X )
NATO
Kungiyar tsaro ta NATO ta lalata wani makami mai linzami da aka harbo daga Iran a gaɓar tekun Bahar Rum yayin da wasu ɓaraguzen makamin s**a faɗo a sassan wurin inji ma'aikatar tsaron Turkiyya. ( Al'Arabiyya News )
TURKEY - NATO
Turkiyya tace Nato ta sake kakkaɓo wani makami mai linzami na Iran a karo na biyu, "abinda ake fargabar cewa wani tarko ne na kokarin shigar da Nato yaƙin" ( Reuters )
AMURKA - TEHRAN
Jaridar Middle East Monitor ta wallafa wani faifan Videon harin Amurka a wata makaranta a Iran wanda aka rawaito a kalla yara 175 sun mutu, abinda Amurka tace adadin bai kai haka ba. ( Middle East Monitor )
UKRAINE
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce kasashe 11 sun nemi taimakon Kyiv kan yadda za a dakile jiragen saman Iran marasa matuka, wadanda Tehran ta harba a duk fadin Gabas ta Tsakiya a matsayin ramuwar gayya ga hare-haren
24/05/2024
Memory 💥
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Address
Kanawa, Kirfi
Bauchi