Labari Daga Bauchi

Labari Daga Bauchi

Share

10/07/2026

KAI TSAYE...

Yanzu haka shugaban masu ruwa da tsakin jam'iyar PRP na karamar hukumar Bambam Alh Salisu Idris Dambam ya Kira taron mutanen Dambam mazauna Bauchi dan wayar masu dakai Kan tafiyar Sanata Shehu Buba Umar a zaben 2027

10/07/2026

SANARWA TA MUSAMMAN

Haɗaɗɗun Ƙungiyoyin Fulani na Bauchi Sun Amince da Naɗin Mallam Aliyu IG a Matsayin Shugaban M.A. RUGA-RUGA Contact Forum 2027

Haɗaɗɗun Ƙungiyoyin Fulani na Jihar Bauchi sun bayyana amincewarsu da naɗin Mallam Aliyu IG a matsayin Shugaban M.A. RUGA-RUGA Contact Forum 2027.

A cikin sanarwar da ƙungiyoyin s**a fitar, sun ce an yi naɗin ne bayan tattaunawa da amincewar shugabanni da wakilan ƙungiyoyin Fulani daga sassa daban-daban na jihar, domin ƙarfafa haɗin kai da kuma inganta ayyukan wayar da kan al’umma a ruga-rugan Fulani da ƙauyukan makiyaya a faɗin Jihar Bauchi.

Sanarwar ta ƙara da cewa dandalin zai mayar da hankali wajen wayar da kan al’umma tare da tallata manufofi da jagorancin Mai Girma Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, H.E. Mohammed Abdullahi Abubakar, SAN (Makama Babba), wanda ake bayyana a matsayin ɗan takarar kujerar Gwamnan Jihar Bauchi a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar APC a babban zaɓen shekarar 2027.

Ƙungiyoyin sun kuma yi kira ga ɗaukacin al’ummar Fulani da sauran magoya bayan APC da su bai wa wannan yunƙuri cikakken goyon baya, tare da nuna haɗin kai domin cimma manufofin da aka sa gaba a zaɓen 2027.

10/07/2026

APC Ta Rantsar da Sabon Shugaban Jam'iyyar a Karamar Hukumar Bauchi

Jam'iyyar APC reshen Jihar Bauchi ta rantsar da Alhaji Nura Abdulwahab Zungur a matsayin sabon Shugaban Jam'iyyar APC na Karamar Hukumar Bauchi.

An gudanar da bikin rantsuwar ne a dakin taro na Jam'iyyar APC na Jihar Bauchi, inda manyan jiga-jigan jam'iyyar, shugabanni da mambobi s**a halarta domin shaidawa da kuma taya sababbin shugabannin murna.

Baya ga Alhaji Nura Abdulwahab Zungur, an kuma rantsar da Hon. Musa Gubi a matsayin Ex-Officio na Jam'iyyar APC a Jihar Bauchi.

Shugaban Jam'iyyar APC na Karamar Hukumar Bauchi, Hon. Tilde, ne ya jagoranci bikin rantsuwar, yayin da Babban Mai Taimakawa Jam'iyyar kan Harkokin Shari'a ya gudanar da rantsar da sababbin shugabannin.

Taron ya gudana cikin lumana tare da nuna haɗin kai tsakanin shugabanni da mambobin jam'iyyar, inda mahalarta s**a bayyana fatan cewa sababbin shugabannin za su yi aiki tukuru wajen ƙarfafa jam'iyyar da kuma bunƙasa harkokinta a Karamar Hukumar Bauchi da ma Jihar Bauchi baki ɗaya.

Want your business to be the top-listed Media Company in Bauchi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


DADA Plaza, OPPOSITE FARIYA FOUNDATION
Bauchi
ABUBAKARUMARSTATESECRETARIAT740261