Zauren Addini
23/09/2023
INA da tambaya.
Mace CE tana cikin Maulidi sai Jini ya tsinko Mata, Shin ya matsayin Maulidin ta.
16/05/2023
```Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuh.๐ค```
_Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!!_
```*Addini A Yau*```
*Na farin cikin gayyatar ilahirin al'ummar musulmai zuwa wajen gagarumin muhadara da za'a gudanar karo na hudu (4)*
*Rana* ```Ranar Laraba 17/05/2023.```
*Lokaci* ```Bayan sallar Magriba.```
*Wuri* : ```Masjid Abu walid Dake sabuwar Unguwan Dumi S/Loda Bauchi, Bauchi State.
```
*Allah ya bada ikon halarta Ameen Thumma Ameen๐๐ป*
*Sanarwa daga*
*Othman Al-jahuniy PRO 3*
AddAddini A YauYAddini A YauuAddini A Yau
15/05/2023
Shin za a iya cewa: Shehu Inyas ya yi rashin uslubi (su'ul adabi) ga Annabi (saw), shi kuma dan gidan Ado Musa ya kaskantar da Annabi (saw)?
Shi Inyas ya yi amfani da kalma mai iya daukar ma'anar kaskantarwa a hakkin Annabi (saw), a fadinsa:
ูู
ุง ููุฏ ุงูุฑุญู
ู ููู ุนุจูุฏู...
Inyas ya yi amfani da kalmar "ุนุจูุฏู" a hakkin Annabi (saw), wacce "Tasgiri" ce na kalmar "ุนุจุฏู". Wato nuna kankantar abu. Ko da an ce ana yin "Tasgiri" bisa manufa ta girmamawa, to ai ana amfani da "Tasgiri" bisa manufa ta kaskantarwa, kuma shi ne asali.
Don haka cewa "ุนุจูุฏู" kalma ce mai rikitarwa, wacce amfani da ita a hakkin Annabi (saw) rashin ladabi ne. Saboda kasancewarta kalma ce mai rikitarwa shi ya sa dan gidan Ado Musa Tafawa Balewa ya rikice, ya fassara baitin da cewa:
"Allah bai haifu ba, amma Annabi a bayin ma KARAMI ne a bayin Allah!".
Sai ya ce:
"Ma'ana shi KANKANIN bawon Allah ne".
Sai ya kaskantar da Annabi (saw).
To me ya sa shi Inyas bai yi amfani da kalmar "ุฎูููู" ko "ุญุจูุจู" ko waninsu a maimakon "ุนุจูุฏู" ba?!
Alhali kalmar "ุฎูููู" ko "ุญุจูุจู" ko "ุฑุณููู" ko "ูุจูู" kowace kalma a cikinsu za ta zauna a gurbin "ุนุจูุฏู", kuma wazanin bai samu matsala ba. Wato ba a samu karyewan baitin ba.
Don haka ko shakka babu, amfani da kalmar "ุนุจูุฏู" a hakkin Annabi (saw) da Inyas ya yi, ko da a bisa manufar girmamawa ne AMFANI NE DA MUMMUNAN USLUBI, DA "SU'UL ADABI" wa Annabi (saw).
Shi ya sa daga cikin rashin uslubi NA SHARI'A akwai yin watsi da lafuzan Shari'a, da dauko lafuza masu rikitarwa, masu harshen damo, ko wadanda s**a saba Shari'a, a zo ana amfani da su a hakkin Allah da Manzonsa (saw). Kuma da ma wannan shi ne Manhajin 'Yan bidi'a. Ba sa takaituwa da lafuzan Shari'a wajen siffanta Allah da Manzonsa (saw), sai dai su yi amfani da lafuzan da s**a ga dama, ko da sun kunshi munanan ma'anoni na kaskantarwa, kamar ita wannar kalma da Inyas ya yi amfani da ita a hakkin Annabi (saw), shi kuma dan gidan Ado Musa - saboda jahilci da zumudi - ya fassara da sifa ta kaskantar da Annabi (saw).
Shi ya sa hanyar Ahlus Sunna ita ce amfani da lafuzan Shari'a:
ุงูุชุนุจูุฑ ุนู ุงูุญู ุจุงูุฃููุงุธ ุงูุดุฑุนูุฉ ุงููุฑุขููุฉ ุงููุจููุฉ ุทุฑููุฉ ุฃูู ุงูุณูุฉ ูุงูุฌู
ุงุนุฉ.
A Nassoshin Shari'a an siffanta Annabi (saw) da "ุนุจุฏ ุงููู" da "ุฑุณูู ุงููู" da "ูุจู ุงููู" da "ุฎููู ุงููู", amma saboda bin Manhajin bidi'a, kai Inyas ka zo ka ce: "ุนุจูุฏู", har ya kai ga mabiyinka dan Ado Musa - saboda jahilci da zumudi - ya zo ya fassara kalmar da cewa "KARAMI CIKIN BAYIN ALLAH, KANKANIN BAWON ALLAH", kalmomin da babu Hausawa biyu da suke sabani a kan cewa ma'anarsu KASKANTARWA NE A HAKKIN ANNABI (SAW).
Saboda haka, dole a soki Inyas da rashin Uslubi.
Shi kuma dan gidan Ado Musa jahilci da zumudi sun sa ya fadi mummunar magana wa Annabi (saw), YA SIFFANTA ANNABI (SAW) DA KARAMIN BAWAN ALLAH, KANKANI CIKIN BAYIN ALLAH. YA KASKANTAR DA ANNABI (SAW).
Zauren Addini
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Jahun
Bauchi