MMS 2023
06/02/2022
JAMA'A KU SHAIDA
KARIN AJUJUWAN KARATU A MAZABAR DARAZO/GANJUWA DAGA Rep Mansur Manu Soro
An samu karin ajujuwan karatu daga gwamnatin tarayya zuwa mazabar mu ta Darazo/Ganjuwa ga fasalin yadda abin yake da guraren da za'a gina ajujuwan karatun;
1. Gifted and Talented School Soro; 1 Block Mai ajujuwan karatu guda uku (3)
2. Gifted and Talented School Sade; 1 Bloock mai ajujuwan karatu guda uku (3)
3. Gifted and Talented School Darazo; 1 Block mai ajujuwan karatu guda uku (3)
4. Gifted and Talented School Kafin Madaki; 1 Bloock mai ajujuwan karatu guda uku (3)
5. Bayan haka Garin Burjitu, Gundumar Kariya 1 Block mai ajujuwan karatu guda (3)
Wannan ayyuka sune cigaban da aka samu a bangaren gine-gine wadda s**a shafi ilimi. Allah ya bada daman kammalawa kuma al'ummar wannan gurare mu anfana.
Malam Mansur Manu Soro Allah ya baka ikon aiwatarwa da dukkan abunda kakeso don cigaban al'umma bakidaya.
02/02/2022
Lanzai tana da border da jahohi guda uku (Borno, Jigawa,Yobe) a dalilin hakane yan gudun hijira s**a yawaita a wannan gari na lanzai kasancewar an samu rashin zaman lafiya a arewacin najeriya.
Wannan yasa ka Rep. Mansur Manu Soro gina makaranta ta SPECIAL PRIMARY SCHOOL LANZAI FOR ORPHANS,IPD's,ALMAJIRI'sa wannan gari na lanzai tare da samar da dukkanin gudummawa daga gwamnatin tarayya wajen ganin wannan makaranta ta tsaya da ƙafarta.
Sannan ya bayar tallafin da yakai kimanin naira miliyan daya domin wannan makaranta ta fara aiki a cikin wannan shekara ta 2022 inshallah, wanda alhamdulillah dukkan tsare tsare sun gama kammaluwa tsakanin maikatar ilimi da kwamiti na makarantar.
Gaskiya idan zamu cire batun siyasa a gefe Rep MMS ya taka rawa matuƙa a fannin ilimi da kiwon lafiya wanda sune damun s**a zama ƙashin bayan na cigaba kowace al'ummah kuma tabbas ya chanchanchi dukkan yabo da karamchi daga al'umma domin yunkurin sa ba iya ɗan APC ko PDP kaɗai yake shafa ba al'umma ne gaba ɗayanta.
Nayi imani wata rana al'umma Darazo/Ganjuwa zasu tabbatar da cewa sun taɓa wakili a majalisar tarayya ko kuma s**e daga Rep MMS aka fara wakilci a majalisar tarayya,wanda mu fatanmu a kullum aiyuka ci-gaba da wanzuwa a wannan yanki namu mai albarka.
Ubangiji Allah ya kara jagoranci Rep MMS allah taimake ka a bisa dukkan yunkurin ka na ganin al'umma ta fita daga halin matsi na rayuwa, ubangiji ya kara himma da tunani mai kyau. Ameen
Aleeyu Darazo
02/02/22
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Bauchi
Bauchi