Intelligent Technology Associates Solutions - ITAS
31/03/2025
GAYYATA TA MUSAMMAN GA MATASAN ITAS/GADAU
Assalamu Alaikum 'yan uwa matasa!
Lokaci yayi da za mu farka daga barcin da muka dade muna yi! Muna rayuwa a duniya mai cike da dama da kuma kalubale, amma idan ba mu tashi tsaye ba, za mu ci gaba da zama a baya. Wannan shine dalilin da ya sa muke gayyatarka/ki zuwa taron "Youth Voices, Challenges and Solutions in Itas/Gadau" – inda matasanmu za mu taru don tattauna matsalolinmu da kuma hanyoyin da za mu bi don ciyar da yankinmu gaba.
Me yasa wannan taro yake da mahimmanci?
1. Lokacinmu ne! Dole ne mu fahimci cewa babu wanda zai gina mana makomar da muke so, sai mu da kanmu.
2. Matasan Itas/Gadau suna fuskantar kalubale iri-iri – Rashin hadin kai, rashin jagoranci, da rashin hanyoyin dogaro da kai.
3. Taron nan dama ce don mu hadu, mu tattauna, mu tsara yadda za mu magance matsalolinmu.
Me za ka amfana da halartar taron?
✅ Zaka fahimci muhimmancin hadin kai da yadda zai taimaka mana mu tashi tsaye.
✅ Zaka samu shawarwari daga kwararru akan yadda za ka shawo kan kalubalen rayuwa.
✅ Zaka fahimci yadda fasaha zata iya zama hanya ta samun ci gaba da dogaro da kai.
✅ Zaka hadu da matasa masu tunani irin naka don mu hada kai mu kawo ci gaba ga yankinmu.
Manyan batutuwan da za a tattauna:
🟢 Karfi a Hadin Kai – Engr. Abdulhakeem Barnoma
🟢 Rashin Jagoranci da Mentorship – Dr. Yahaya Saad Itas MNSPS
🟢 Kalubalen da Matasanmu Ke Fuskanta – Alh. Hamisu Aliyu Shamaki
🟢 Matasa da Fasaha: Gano Basirarka, Sauya Tunani, da Gina Makomarka – Nura Said
Cikakken bayani kan taron:
📍 Wurin taro: GGDSS Itas
📆 Ranar taro: 1 ga April, 2025
⏰ Lokaci: 10:00AM
Muna fatan ganin ka domin mu hada kai, mu tattauna hanyoyin da za mu inganta yankinmu da kuma rayuwarmu! Kar ka bari a ba ka labari!
27/03/2025
INVITATION TO A SPECIAL PROGRAMME ON YOUTH VOICES, CHALLENGES, AND SOLUTIONS IN ITAS-GADAU
The Itas-Gadau Youth Forum, in collaboration with the National Association of Itas-Gadau Students (NAIGAS) and Intelligent Technology Associates Solutions (ITAS), invites you to a vital discussion on youth development, challenges, and solutions in Itas-Gadau.
Event Details:
📅 Date: Tuesday, 1st April 2025
🕘 Time: 10:00 AM
📍Venue:GGDSS Itas
Why Attend?
✅ Engage in impactful discussions on education, employment, and digital opportunities.
✅ Discover practical solutions and strategies for youth empowerment.
✅ Network with community leaders, experts, and like-minded young people.
Join us in shaping the future of Itas-Gadau by raising your voice, sharing ideas, and working towards sustainable solutions. Together, we can build a brighter future!
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Bauchi