Naziru Musa
23/05/2026
Sufanci itace mafita a wannan zamanin muddin mutum ya riƙeta zai samu tsira saboda Istigfari da hailala da salati annabi sallallahu alaihi wassallam..
Domin yadda zamanin mu ta lalace ayyukan mu s**a munana idan bada tuba da neman kusanci da allah ba akwai babban matsala
Allah dai yasa muyi kyakyawan ƙarshe ameeen.
23/05/2026
Gaskiya ce a harshen su, ya kamata ce a aikin su, nagarta ce a dabi'arsu, soyayya domin Allah ne muradinsu, Allah ya tsare su irin tsarewar da ke yiwa waliyansa, ya jiɓinci lamuransu irin jibintar da yake yiwa bayin da s**a koma zuwa gare shi, Allah ya daukaka ambaton su irin daukakawar da yake yiwa bayin da s**a bi shi....
Allah ka mana shaida da muna son su saboda kai, kasa wannan soyayyar ta mana anfani, ka sa mu zama na kusa da su a duniya da lahira...
Albarkacin Annabi da Alkur'ani.
Abul Abbas.
23/05/2026
Kar ka zamto Dalilin fa'dawar wani cikin masifa, don zai kasance tsawon rayuwarsa, da zaran ya ji an ambaci labarinka, sai ya fara maimaita: HASBIYALLAHU WA NI'MAL WAKEEL... Hakan zai zamto tamkar ya na aika wasu Boma-Bomai ne gareka.
22/05/2026
ALQUR'ANI, LITTAFI MAI BAN MAMAKI
📘📘📘📘📘📘📘📘📘📘📘📘📘📘📘
“Alqur'ani zancen Allah ne, Shi ne Ya fare shi ba tare da an san yadda Ya furta shi ba, kuma Ya saukar dashi ga AnnabinSa ta hanyar wahayi, kuma lalle ne tabbas Muminai sun gaskata shi, kuma sun sakankance da cewa haƙiƙa Zance ne na Allah (S.W.T.), ba halittaccen abu ba ne kamar zancen halittunsa, duk kuma wanda ya ji shi sa,an nan ya riya cewa zancen mutum ne, to, lalle ne ya kafirta....”
Wanda Ya saukar da shi (S.W.T.) Ya sifanta shi, inda Yake cewa:
وإنه لكتاب عزير * لا يأتيه الباطل من بين يديه ولا من خلفه تنزيل من حكيم حميد
"Kuma lalle shi, hakika, Littãfi ne mabuwãyi. ɓarna bã zã ta je masa ba daga gaba gare shi, kuma bã zã ta zo ba daga bãya gare shi. Saukarwa ce daga Mai hikima, Godadde. (Suratul Fussilat 41-42).
Kamar yadda Allah Mai bayyanannar Kudura Ya sifanta shi, Yana cewa:
كتاب أحكمت ءاياته ثم فصلت من لدن حكيم خبير
"Littãfi ne an kyautata ãyoyinsa, sa'an nan an bayyana su daki-daki, daga wurin Mai hikima, Mai Kididdigewa." (Suratu Hud: 1).
Lalle ne: Haƙiƙa ayoyin Alqur'ani mai tsarki suna cikin tabbataccen tsari matuka, da kuma cikakken bayani wanda Mai hikima Ya kyautata tsarinsu, sa'an nan Gwani Ya rarrabe su daki-daki, kuma haka wannan Littafi zai ci gaba da kasancewa gagara-koyo ta ɓangaren zurfin balaga, hukunce-hukunce, ilimi, tarihi da wasunsu, har zuwa lokacin da Allah zai gaji duniya da abinda ke cikinta, babu wani abu na canji da zai shigo masa komin kankantarsa, hakan na gaskata zancen Allah (S.W.T.) Cewa:
إنا نحن نزلنا الذكر وإنا له لحافظون
"Lalle Mu ne, Muka saukar da Ambato (Alqur'ãni), kuma lalle Mu, hakika, Mãsu kiyãyewa ne gare shi" (Suratul Hijr: 9)
ALLAH YA SANYA MU CIKIN MASU RIQO DASHI DA AIKI DA KARANTARWARSA, AMEEEN.
22/05/2026
An Sanyawa Wani Layi Sunan Shehu Ibrahim A Amuruka
A nan ɗaya ne daga cikin jikokin maulanmu Shehu Ibrahim Inyass ke tsaye akan layi mai suna Barham street a Detroit Michigan a ƙasar Amuruka...
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Bappajo Road Bauchi
Bauchi