Alhassan Beli
14/04/2025
YA KASHE MATARSA SABODA TAKI KARBOWA RANCE KUDI A BANKI TA BASHI
Wani magidanci a birnin Makka a kasar Saudi Arabia ya kashe matarsa mai suna Rehab Alzahrani mai shekaru 28.
Mijin nata ya bukaci ta karbo rancen riyal 400,000 ne a banki da sunan ta, ta bashi yayinda ita kuma taki amincewa yanda hakan ya janyo mijin nata ya lakaɗa mata duka, inda ita kuma ta koma wajen mahaifiyar ta s**a kai rohoton mijin wajen ƴan sanda.
Ƴan sandan sun sasanta su yayinda ta kara komawa gidan mijin, bayan komawar ta ne sai mijin ya kara far mata, inda ya watsa mata guba, yayinda makwafta s**a kawo mata dauki ne sai mijin ya ringa musu barazana, sai dai duk da haka basu yi kasa a gwiwa ba sun ceci matar inda s**a kaita asibitin Al Noor dake cikin birnin Makka.
Kafin numfashin ta na karshe Rehab tace da maifiyar ta "Ki kulamin da wannan yarinyar"
Rehab ta rasu sannan anyi mata sallah a masallacin Harami inda daga nan aka dauke ta maƙabartar Haram E Shuhada.
Yanzu haka dai ƴan sanda a birnin Makka sun cafke mijin.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Azare