Anka24 Tv Channel

Anka24 Tv Channel

Share

Photos from Anka24 Tv Channel's post 30/04/2026

JAM’IYAR PDP RESHEN KARAMAR HUKUMAR MULKI TA ANKA TA GUDANAR DA TARON KADDAMAR DA SHUWAGABANNIN PARTY MATAKIN GUNDUMA A YAU ALHAMIS 20/APRIL/2026

Photos from Anka24 Tv Channel's post 15/04/2026

ZANNAN SUPPORT GROUP ANKA

GAMAYYAR KUNGIYOYIN GIDAN ZANNAN BUNGUDU DAKE GARIN ANKA SUNYI MUBA'AYI GA MAIGIRMA GWAMNA DAUDA LAWAL DARE.

A wani mataki na tabbatar da umarnin Maigirma HON Dr Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu ga daukacin kungiyoyi da magoya bayansa dake kananan hukumomi goma-sha hudu na jihar Zamfara, gamayyar manyan kungiyoyin gidan Zannah guda (6) da s**a hada da:

1.Zannah Support Group.
2.Zannah Like-maind.
3.Zannah Solidarity.
4.Zannah Muke Fata.
5.Zannah Connect.
6.Zannah Trust.

Sun jaddada umarnin His-Excellency Hon.Dr. Abdulmalik Zubairu Bungudu na goyon bayan Maigirma Gwamna Dr. Dauda Lawal karo na biyu ta hannun wakilin Maigirma Gwamna Shugaban karamar hukumar mulkin Anka Hon bello tungar kuda kuku a dacin taro dake cikin sakatariyar karamar hukumar mulkin Anka

Da yake gabatar da jawabi amadadin dukkanin shuwagabannin kungiyoyin Hon. Shafii musa sarkin yamman anka da Malan Abdullahi Garba Anka sun bayyana cewa, daga yau duk wata hidima da ta shafi nasarar Maigirma Gwamna Dr Dauda lawal dare ashirye wadannan gamayyar kungiyoyi suke domin bada gudunmuwar su bisa umarnin mai girma Hon Dr Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu.

Shima da yake maida jawabi a wurin taron, Maigirma Mukaddashin Shugaban karamar hukumar mulki ta ank Hon bello tungar kuda kuku ya bayyana jindaɗinsa bisa wannan muba'ayi, tare da bayyana Zannan Bungudu amatsayin dan siyasa mai matukar anfanar da al-ummar jihar Zamfara, inda ya bada tabbacin yin aiki kafaɗa-da-kafaɗa da mutanen Zannah dake Karamar hukumar mulki ta anka

Taron ya samu halartar dukkanin shuwagabannin kungiyoyin da mambobin su, Wakilan Jam'iyyar APC, Dattawa, da sauran yan Jam'iyya Maza da mata, Allah (SWT) ya kara karfafa wannan tafiya ta Zannah, Allah ya taimaki Gwamnatin Zamfara da al-ummar Zamfara baki daya Allahumma Amin.

13/04/2026

Daga Fadar Mai Martaba Sarkin Zamfara Yayinda Dan Takarar Dan Majalisar Anka Da Kewaye Yakai Ziyarar Bangirma Tare Da Neman Addu’a Da Saka Albarka Daga Bakin Mai Martaba

Want your business to be the top-listed Media Company in Anka?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address


Anka, Magaji Ward
Anka