Arewa Post

Arewa Post

Share

Photos from Arewa Post's post 04/05/2026

Ɗan Tsohon Shugaban Kasa, Honarabul Yusuf Buhari Yana Cigaba Da Tattaunawa Da Al'ummar Mazaɓar Majalisar Tarayya Daura Da Sandamu Da Kuma Maiaduwa A Jihar Katsina

28/04/2026

Kungiyar “Arewa Media Writers” Ta Yi Allah-Wadai da Amincewa Da Sabon Bashin Dala Miliyan 516.3 Domin Aikin Titin Sokoto–Badagry

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” ƙarƙashin jagorancin Comr Haidar Hashim Kano, ta yi Allah-wadai da matakin da Majalisar Wakilai ta ɗauka na amincewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓo bashin dala miliyan 516.3 domin aikin titin Sokoto–Badagry.

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce wannan mataki na ƙara ɗora wa ƙasar nan nauyin bashi a daidai lokacin da tattalin arziƙin al’umma ke cikin mawuyacin hali, abin da ke haifar da damuwa kan makomar tattalin arziƙin Najeriya.

Ƙungiyar ta jaddada cewa yawan karɓar bashi ba tare da cikakken bayani kan hanyoyin biyan sa da kuma tasirin sa ga rayuwar al’umma ba na nuna rashin tsari da hangen nesa daga bangaren gwamnati da majalisun dokoki.

“Abin takaici ne yadda ake ci gaba da ɗaukar irin waɗannan matakai ba tare da la’akari da halin ƙunci da talauci da al’umma ke ciki ba. Wannan na ƙara tsananta wahalhalun da jama’a ke fuskanta a yau,” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda Majalisar Dattawa ta amince da irin waɗannan shirye-shirye ba tare da zurfin nazari da la’akari da ra’ayin al’umma ba, lamarin da ta ce bai dace da tsarin dimokuraɗiyya ba.

Ta ƙara da cewa ci gaba da jingina ci gaban ƙasa da bashin ƙasashen waje na iya jefa Najeriya cikin matsin tattalin arziƙi a nan gaba, tare da barazana ga ‘yancin tattalin arziƙin ƙasar.

Don haka, “Arewa Media Writers” ta bukaci Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dattawa da su sake nazari kan wannan mataki, su fifita hanyoyin inganta tattalin arziƙi cikin gida ba tare da dogaro da bashin waje ba.

A ƙarshe, ƙungiyar ta yi kira ga al’umma da su kasance masu lura da irin waɗannan matakai tare da riƙe shugabanni da alhakin duk wata doka ko shawara da za ta shafi rayuwarsu.

Comr. Muhammad Kwairi Waziri
National Editor I, Arewa Media Writers

Want your business to be the top-listed Media Company in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Nsukka Street Abuja
Abuja