Fim Magazine
09/05/2026
Dakaru sun ga bayan ’yan ta’adda masu yawa, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro
Rundunar Tsaro ta Kasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun kasar nan sun samu nasarar ragargazar dimbin ’yan ta’adda, inda s**a k**a wasu da dama tare da ceto mutum sama da 50 da aka yi garkuwa da su a fadin kasar nan.
Wadannan nasarori sun faru ne a yayin ayyukan kakkaba da sojoji s**a gudanar tsakanin ranar 30 ga watan Afrilu zuwa 7 ga watan Mayun 2026.
Daraktan Yada Labarai na Rundunar Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja. Ga yadda nasarorin suke kasance a kowacce shiyya:
• Arewa maso Gabas (Operation HADIN KAI): Rundunar ta dakile hare-haren ’yan ta’adda a Magumeri da ke jihar Borno. Haka kuma, wasu daga cikin maharan sun mika wuya, yayin da aka k**a masu kai musu kayan abinci da mak**ai.
• Arewa maso Yamma (Operation FANSAN YAMMA): Sojoji sun yi artabu da ’yan fashi a jihohin Katsina da Zamfara, inda aka kashe da dama tare da kwace babura da mak**ai.
• Arewa ta Tsakiya (Operation SAVANNAH SHIELD): An ceto wadanda aka yi garkuwa da su tare da k**a masu safarar harsasai har guda 250 a cikin birnin Abuja.
• Jihar Filato: Jami'an tsaro sun bankado wata masana’antar kera mak**ai ba bisa ka’ida ba a Jos ta Kudu, inda aka k**a mutanen da ake zargi da kera bindigogi.
• Jihar Benuwai da Kogi: An samu nasarar ceto wasu yara dalibai da aka sace daga gidan marayu.
Janar Onoja ya kara da cewa, dakarun Operation DELTA SAFE a Kudancin kasar da kuma Operation UDO KA a Kudu maso Gabas duk sun samu nasarar k**a masu garkuwa da mutane da kuma dillalan mak**ai na kungiyar IPOB/ESN.
"Rundunar sojin kasa a karkashin jagorancin Shugaban Hafsun Tsaro, Olufemi Oluyede, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa ’yan Najeriya sun rayu cikin lumana da kwanciyar hankali." — Maj. Gen. Onoja
Wannan gagarumar nasara ta nuna cewa jami’an tsaro sun sake zage damtse wajen ganin sun kawo karshen matsalolin tsaro da s**a addabi sassan kasar nan.
08/05/2026
Ƙwaƙudumar kasa biyan tulin bashin da manyan bankuna s**a bayar laifin daraktoci da manyan masu hannayen jarin su ne, ba laifin CBN ba
Ashafa Murnai Barkiya
Yayin da ake fama da gagarumar matsalar yawan maƙudan kuɗaɗen da bankuna s**a bayar bashi, kuma biyan bashin ya gagara, akwai masu ɗora laifin kan Babban Bankin Nijeriya (CBN), a matsayin sa na mai kula da kuma sa-ido kan dukkan bankunan Nijeriya.
To sai dai kuma idan aka yi la'akari da yanayin yadda manya da ƙananan bankuna ke bayar da basuss**an, to fa dole ne kacokan a ɗora laifin kan daraktocin bankunan da matsalar ta shafa da kuma manyan masu zuba jari a bankunan.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da CBN ya bada umarni ga wasu bankuna cewa kada su raba ribar ƙarshen shekara-shekara, saboda ɗimbin bashin da bankunan s**a bayar, wanda ba a biya ba, har ya riƙe wa bankunan wuya.
A irin wannan tsomomuwar bashin ne kamfanin ɗanyen mai da iskar gas, Nestoil mallakar Ernest Obiejesi ya ci bashin Naira Tiriliyan 2.9 a hannun wasu manya da ƙananan bankunan Nijeriya.
Masu Hannun Jari Ba ‘Yan Kallo Ba Ne:
A ƙarƙashin Dokar Kamfanoni da Harkokin Kasuwanci ta 2020 (CAMA 2020), masu hannun jari ba ‘yan kallo ba ne kawai, su ne ke da cikakken iko a harkokin shugabanci. Sashe na 238 ya bai wa taron gaba ɗaya iko, yayin da sashe na 271 zuwa 274 ke tanadin yadda ake naɗawa, cirewa da kuma biyan daraktoci.
Wannan yana nufin masu hannun jari ne ke zaɓar waɗanda za su tafiyar da banki, su kuma amince da albashin su da ladar su—wannan kuwa yana tasiri kai tsaye ga yadda suke gudanar da aiki.
Sashe na 238 ba kawai ƙa'ida ba ce, ginshiƙi ne na gaskiya da ɗaukar nauyi. Yana tabbatar da cewa masu kamfani ne ke zaɓar shugabanni, yana hana ƙungiyoyin daraktoci zama masu cin gashin kan su ba tare da kulawa ba. Haka kuma yana tabbatar da gaskiya a cikin tsarin naɗi, yana rage yiwuwar nadin ɓoye ko na son zuciya.
Wannan tsarin yana ƙarfafa ɗaukar alhaki, domin daraktoci sun san cewa masu hannun jari ne s**a zaɓe su kuma za su iya cire su idan sun gaza.
Haka kuma yana taimaka wa masu kula (regulators) su san wane ne ke jagoranci da kuma yadda aka kai ga hakan.
A lokacin rikici, wannan sashe yana nuna cewa daraktoci ba su zo ne bisa kuskure ba—an zaɓe su ne da niyya, don haka dole a duba har da rawar masu hannun jari.
Amma a aikace, sau da yawa masu hannun jari kan goyi bayan faɗaɗa bayar da bashi domin samun riba mai yawa a lokacin bunƙasa tattalin arziki, sai kuma su koma baya su ɗora laifi kan wasu idan abubuwa s**a lalace. Wannan hali yana haifar da matsala.
Daraktoci Sun Rigaya Sun Fuskanci Tsauraran Dokoki:
Ra’ayin cewa daraktoci ba su da alhaki a doka ba gaskiya ba ne. CAMA 2020 ya fayyace wajibai:
Sashe na 305 ya fayyace cewa: Wajibi ne daraktoci yu yi aiki cikin gaskiya don amfanin kamfani.
Sashe na 306: Su yi aiki da ƙwarewa da kulawa.
Sashe na 309: Su guji rikicin son-kai, son-rai da son-zuciya.
Haka kuma dokar bankuna ta BOFIA 2020 ta ƙara tsaurara wannan:
Sashe na 19 ya ce: Dole ne a bayar da bashi bisa ƙa’idojin banki masu kyau da fa'ida.
Sashe na 20: Ya hana bayar da bashi ga masu alaƙa da masu bayar da bashin, ba tare da bin ƙa’ida ba.
Idan aka karya waɗannan dokoki, akwai hukunci ciki har da tara, kora ko ma hukuncin kotu.
Saboda haka, tsarin doka ya riga ya tanadi yadda za a ɗauki mataki. Ba duk wani bashin da ya lalace ne sak**akon laifi ba—banki kasuwanci ne mai haɗari.
CBN Na Aiki Cikin Tsarin Da Doka Ta Gindaya:
Masu s**ar CBN suna mantawa cewa Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Hadahadar Kuɗi, wato 'Banks and Other Financial Institutions Act' (BOFIA 2020), ta tanadi yadda za a ɗauki mataki a hankali:
Sashe na 33: Ya hana rabon riba da ƙari don kare jarin banki.
Sashe na 34: Ya bada damar cire daraktoci amma sai da hujja mai ƙarfi.
Wannan yana nuna cewa matakan suna zuwa ne a hankali:
Kariya kafin hukunci:
Dakatar da rabon ribar ƙarshen shekara-shekara da aka yi yanzu wata hanya ce ta kare tsarin banki, ba rauni ba ne. Wannan ya yi daidai da ƙa’idojin ƙasashe na duniya.
Shugabanci Tsari Ne Na Haɗin Gwiwa:
Shugabancin banki a yau ya haɗa da ɓangarori da dama:
Daraktoci, masu hannun jari, masu bin-diddigin lissafi, wato 'auditors', kwamitocin duba afkuwar matsala da tantance bashi.
Daraktoci masu zaman kan su suna taka muhimmiyar rawa wajen hana almubazzaranci.
Wasu Matsalolin da ke Haifar da Kasa Biyan Bashi ga Bankuna:
Rikicin bashin da ya faskara a biya, wato 'bad bebt', yana da alaƙa da:
Sauyin farashin kayayyaki, matsalar canjin kuɗi, raunin tsarin tattalin arziki da sauran su.
Idan manyan masu karɓar bashi sun gaza biya, tasirin yana shafar dukkan bankuna.
Buƙatar Tsari Mai Ɗorewa:
Masu hannun jari su riƙa taka rawar gani. Daraktoci su bi dokoki da ƙa’idoji. Tsarin bankuna ya ƙarfafa ɗabi’a mai kyau. CBN ta ci gaba da aiki cikin doka, k**ar yadda a yanzu yake maida himma kan haka ɗin.
A ƙarshe, ɗora laifi kacokan kan CBN kawai ba daidai ba ne. Tsarin doka ya riga ya rarraba alhaki tsakanin:
Masu hannun jari, daraktoci, masu gudanarwa.
A duk inda aka samu laifi, to akwai hukuncin da doka ta tanada. Amma inda matsalar ta samo asali daga yanayin tattalin arziki, dole ne a ɗauki mataki cikin hikima.
Abin da ɓangaren banki ke buƙata ba zargin juna ba ne, sai dai tsarin gaskiya da ɗaukar alhaki daga kowane ɓangare—tun daga hukumar daraktocin banki, har zuwa masu hannun jari. Idan ba a yi haka ba, ko wane irin tsauraran matakan da aka ɗauka ba za su kawo canji mai ɗorewa ba.
Yadda ƙarfin laƙani da dafa'in CBN ke hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana
Daga Ashafa Murnai Barkiya
Manyan sauye-sauyen da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya aiwatar, sun zama ƙaƙƙarfar kariya ga girgizar tattalin arzikin duniya, suna kuma taimakawa wajen tabbatar da amincewar masu zuba jari da kuma ƙara hasashen bunƙasar tattalin arziki.
Sauye-sauyen da CBN ƙarƙashin jagorancin Olayemi Cardoso ya gabatar sun shirya tattalin arzikin ƙasar don jure ƙalubalen da ke tasowa daga waje, ta hanyar samar da matakan kariya da ke tabbatar da ɗorewar tattalin arziki. Shugabannin kasuwanci na cikin gida da na ƙasashen waje sun amince cewa yanzu Nijeriya na da kyakkyawan matsayi don tunkarar girgizar tattalin arziki daga waje, tare da ci gaba da samun amincewar masu zuba jari.
Daidaituwar farashin canjin kuɗi da ci gaba da shigowar kuɗaɗen waje cikin asusun ajiyar ƙasa na bayar da dama mai kyau ga ɗorewar tattalin arziki da bunƙasa mai ɗorewa.
Tattalin arzikin Nijeriya ya samu gagarumin sauyi a ‘yan shekarun nan sak**akon waɗannan gyare-gyare. K**a daga daidaita farashin canjin kuɗi, ƙara tsauraran dokoki, inganta tsarin gaskiya a harkokin kasuwar canjin kuɗi, zuwa ƙarfafa sa-ido kan safarar kuɗi, duk sun taimaka wajen tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.
Muhimmin ɓangare na waɗannan sauye-sauye ya haifar da fa’ida mai yawa ga tattalin arziki, ciki har da samar da kariya don daidaito da bunƙasa tattalin arziki.
Duk da matsin lambar da rikicin Gabas ta Tsakiya ya haifar, tattalin arzikin Nijeriya ya ci gaba da kasancewa mai ƙarfi kuma yana jan hankalin masu zuba jari na duniya.
Masu zuba jari sun ci gaba da neman kadarorin Nijeriya yayin da tasirin sauye-sauyen CBN ke yaɗuwa zuwa muhimman sassan tattalin arziki.
Yadda CBN Ya Fara Gano Laƙanin Bunƙasa Tattalin Arziki:
CBN ta fara aiwatar da tsare-tsare masu ƙarfi don jawo ƙarin jari daga ƙasashen waje da kuma tabbatar da daidaiton farashi da canjin kuɗi. Fiye da shekaru biyu da s**a gabata, gwamnati tare da CBN ƙarƙashin Cardoso sun ‘yantar da kasuwar canjin kuɗi, sun dakatar da bayar da rance kai-tsaye ga gwamnati, sannan aka gyara tsarin tallafin mai.
Haka kuma, gwamnati ta ƙarfafa tara kudaden shiga tare da ɗaukar matakai don rage hauhawar farashi.
Tun bayan aiwatar da waɗannan tsare-tsare, ajiyar kuɗaɗen waje ya ƙaru, kuma mutane na samun damar sayen kuɗaɗen waje cikin sauƙi a kasuwar musayar kuɗaɗe ta hukuma.
Sannan kuma Nijeriya ta sake komawa kasuwannin kuɗaɗe na duniya a watan Disambar da ya gabata, kuma kamfanonin ƙididdiga sun ɗaga darajar ta. Sabon matatar mai na cikin gida mai zaman kan sa yana taimaka wa ƙasar ta ƙara daraja ma'aunin hadahada a duniya.
Manufofin CBN, ciki har da gyaran tsarin hadahadar kuɗi, sun jawo shigowar jari daga ƙasashen waje tare da rage tsoma bakin CBN a kasuwar canjin kuɗi.
Daidaita farashin canjin kuɗi da kuma biyan bashin sama da dala biliyan 7 na kasuwar musayar kuɗaɗe ya ƙara inganta yanayin saka jari, inda Bankin Duniya ya bayyana hakan a matsayin mataki mai ƙarfi don tabbatar da ɗorewar tattalin arziki.
Sannan kuma bambancin haɗarin bashin Nijeriya ya ragu zuwa mafi ƙanƙanta tun daga Janairu 2020, abin da ya nuna ƙoƙarin jawo masu zuba jari da ci gaba da shigar jari daga ƙasashen waje.
Cardoso ya bayyana cewa haɗin gwiwa na da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin tattalin arziki:
“Gudanar da rage hauhawar farashi a yanayin matsin lamba na buƙatar ƙarfafan manufofi da haɗin gwiwa tsakanin ɓangaren kuɗi da na gwamnati, don tabbatar da amincewar masu zuba jari. Dole mu maida hankali kan daidaiton farashi da dawo da ƙarfin nauyin aljihun jama’a.”
Shirin Ƙara Ƙarfin Jarin Bankuna:
CBN ya kuma maida hankali kan ƙarfafa bankuna, inda ya ƙaddamar da sabbin ƙa’idojin ƙarin babban jari ga bankuna daga Maris 2026, domin ƙarfafa su da kuma shirya tattalin arziki zuwa darajar dala tiriliyan ɗaya.
Ƙaruwar Shigowar Jari Daga Ƙasashen Waje:
Cardoso ya bayyana cewa Nijeriya na samun kusan dala miliyan 600 duk wata daga kuɗaɗen ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashe daban-daban. Ya ce sauye-sauyen sun taimaka wajen rage tasirin girgizar tattalin arziki daga waje, tare da inganta kasuwar canjin kuɗi da asusun ajiyar waje.
Ya ƙara da cewa bankunan Nijeriya suna cikin ƙoshin nagarta da inganci, kuma sun samu nasarar tara sabon babban jari don tallafawa bunƙasar tattalin arziki da samar da rance ga ƙananan ‘yan kasuwa.
Rahoton Duba Halin Tattalin Arzikin Nijeriya:
Rahoton 'Global Economic Prospects' na Bankin Duniya ya ɗaga hasashen bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya zuwa kashi 4.4% a 2026 daga kashi 3.7%.
Rahoton ya ce bunƙasar za ta samu ne sak**akon ci gaban sashen ayyuka, farfaɗowar noma, da kuma gyare-gyaren tattalin arziki da manufofin kuɗi masu kyau.
CBN ma ya yi hasashen bunƙasa zuwa kashi 4.49% a 2026, yana danganta hakan da ci gaba da sauye-sauye da sassauta manufofin kuɗi.
Batun Tasirin Rikicin Gabas ta Tsakiya:
Shugabar Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), Kristalina Georgieva, ta ce ƙasashen da ke fitar da mai k**ar Nijeriya za su fuskanci ƙarancin illa idan aka kwatanta da masu shigo da mai.
Rahoton IMF ya nuna cewa rikicin ya shafi duniya baki ɗaya, amma tasirin ya fi tsanani ga wasu ƙasashe fiye da wasu.
Georgieva ta ce:
“Dole ne mu fahimci yadda wannan girgiza ke shafar tattalin arziki da kuma matakan da za su rage raɗaɗin da yake haifarwa.”
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
19 Chelsea Chibuzor Street Off NICON Junction Maitama
Abuja