Explorer Hausa
Yayin da farashin gas ɗin girki ke ci gaba da tashi a Najeriya, iyalai da ɗalibai a jihar Adamawa na kokawa kan yadda lamarin ke ƙara musu tsananin rayuwa.
08/06/2026
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya kai ziyara Uganda yayin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar ɓullar cutar Ebola.
Ziyarar na da nufin duba matakan da ake ɗauka domin dakile yaɗuwar cutar da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.
08/06/2026
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta ceto rayuka 34 tare da kare dukiyoyi da darajarsu ta haura naira miliyan 437 a cikin watan Mayun 2026.
Sai dai hukumar ta ce mutane 13 sun rasa rayukansu sakamakon gobara, haɗuran mota da kuma wasu hatsarori da s**a shafi rijiyoyi da tafkuna.
08/06/2026
Tsohuwar Sanata mai wakiltar Ogun ta Tsakiya kuma ‘yar tsohon shugaban ƙasa, Iyabo Obasanjo, ta sanar da ficewa daga jam’iyyar APC.
A cikin wasiƙar murabus ɗin ta, ta bayyana cewa ta yanke shawarar ce bayan dogon lokaci tana fuskantar abin da ta kira wariya, rashin mutuntawa da kuma nuna mata halin ko-in-kula daga shugabannin jam’iyyar.
Dauki-dora da APC da NDC ke yi a Kano ba ta bani tsoro - Dalhatu
Gwamna Abba na APC da Abdussalam Gwarzo na NDC duk 'yan dauki-dora ne kuma takarar shugabancin Najeriya ta Jonathan a PDP wasan kwaikwayo ne a cewar Muhammad Bello Dalhatu dan takarar gwamnan Kano na PDP a zaben 2027.
Dalhatu ya fadi haka ne a hira ta musamman da Explorer Hausa News
08/06/2026
Gwamnatin China ta fara aiwatar da sabon tsari na wajabta koyar da ilimin fasahar (AI) a dukkan makarantun firamare da sakandare.
Wannan mataki na cikin manyan shirye-shiryen ƙasar na bunƙasa fasaha da shirya matasa domin tunkarar ƙalubalen tattalin arziƙin zamani da ke ƙara dogaro da fasahar kere-kere.
08/06/2026
Jam’iyyar NDC ta sauya wasu daga cikin ‘yan takarar da aka tura daga ɓangaren Kwankwasiyya a Jihar Kano, bayan zargin karya yarjejeniyar rabon iko da aka cimma tsakanin shugabannin jam’iyyar da ƙungiyar Kwankwasiyya.
Rahotanni sun nuna cewa shugabannin NDC a Arewa maso Yamma sun yi korafin cewa an ware mambobin jam’iyyar da ba sa cikin Kwankwasiyya daga tsarin rabon fom ɗin takara da kuma zaɓen ‘yan takara.
08/06/2026
Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya, Peter Obi, ya ce ya fahimci raɗaɗin da Fulani ke fuskanta sakamakon tsangwama da ake yi musu.
Ya bayyana cewa shi ma ya sha fama da irin wannan wariya a matsayinsa na ɗan kabilar Igbo.
Obi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji ɗora laifin wasu tsiraru a kan ƙabila baki ɗaya, yana mai jaddada cewa haɗin kai da adalci su ne hanyar gina ƙasa mai zaman lafiya.
08/06/2026
Shugaban Real Madrid, Florentino Perez, ya sake samun nasara a zaɓen shugaban kungiyar bayan kayar da abokin hamayyarsa, Enrique Riquelme.
Perez ya samu nasara da kashi 65 na kuri’u a zaben da aka yi ranar Lahadi, inda zai ci gaba da jagoranci har 2030.
08/06/2026
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba da sauran masu tayar da zaune tsaye.
Ya jaddada cewa za a ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalolin tsaro domin dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
52 ML Wushishi Crescent
Abuja
900108