DMA - PRESS

DMA - PRESS

Share

25/02/2025

SAƘON TA'AZIYYAR SAYYID HASSAN NA§RÜLLÆH

A madadin Matasan Harƙar Musulunci ƙarƙashin Jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), muna miƙa ta'aziyyarmu ta musamman ga Sahibul Asr (ATFS), Sayyid Qa'id (DZ), jagora Sayyid Zakzaky (H) gami da iyalai da ƴan uwan Shaheed Hassan Næsrųllæh da Sayyid Hashim Safiyyudeen na wannan babban rashi.

Saƙon ta'aziyyarmu ga ɗaukacin iyalan waɗannan Shahidai masu girma, tare da sauran al'ummar duniya (Musulmi da Kirista) gami da raunana na rashin waɗannan waɗanda s**a kasance garkuwa garemu baki ɗaya.

Duk da cewa waɗannan Shahidai ba sa cikinmu a zahiri, amma muna da yaƙinin suna tare da mu a baɗini, kuma muna nan a kan turbarsu, sannan za mu tabbar wa Yahudawa cewa har yanzu Sayyid Hassan bai mutu ba, kuma za su ga hakan a zahiri.

A ƙarshe muna roƙon Allah (SWT) da ya karɓi shahadar Sayyid Hasan Næsrüllæh da ɗan uwansa Shaheed Sayyid Hashim Safiyyuddin tare da sauran shahidan gwagwarmaya baki ɗaya, Allah (T) ya ɗaukaka darajarsu.

Youth Forum Media Team
Ja'afar Mustapha Sarina
A madadin Dandalin Matasa
25 - 02 - 2025

02/02/2025

-Ga Wani Sirri da Ake Yinsa A Cikin Wannan Watan Na Sha'aban.

-An Ruwaito Daga Imam Ali (AS) Shi Kuma Yaji Daga Manzon Allah (S) Yace: "Duk Wanda Ya Karanta Waɗannan Surorin A Cikin Wannan Wata Na Sha'aban Allah Zai Biya Masa Dukkan Buƙatunsa Kuma Ya Gafarta Masa Dukkan Zunubansa.

-Ga Surorin Kamar Haka:

-(1) Surar Fatiha, ×3
-(2) Ayatul Qursiyyu,×3
-(3) Kulya-Ayyuhal- Kafirun, ×3
-(4) Kulhullahu-Ahad, ×3
-(5) Kul A’uzu Birabbil Falak, ×3
-(6) Kul A’uzu Birabbin Nas, ×3

-Bayan An Kammala Karantawa Sai A Roƙi Allah Dukkan Buƙatun da Ake Nema, Cikin Gaggawa Za'a ga Biyan Buƙata.

-Ana Karantawa A Dukkanin Ranakun Sha'aban.

-Muhammad Jiddah Nguru
07037009525

31/01/2025

اللهم صلى على محمد وآل محمد 💖💗
Allahumma salli ala Muhammad wa Ali Muhammad wa ajjil farajahum

Want your business to be the top-listed Media Company in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Abuja