AWAINIYA.com
02/06/2026
DAN BAIWA Ya gina robot din gona da zai taimakawa manoma wajen gano kwari da maganin su a ganye… amma wannan ba shine abin mamaki ba
Wannan robot din yana tafiya da kansa (Autonomous)
Yana amfani da AI wajen gane ganye
Yana duba ko akwai kwari
Idan ya gano su… sai ya fesa magani nan take
Idan babu… sai ya cigaba da tafiya k**ar komai
Amma sedai wannan prototype ne kafin na production
Ina da babban burin yaje international
Label amma tere da kokarin ku ne zaiyu ka iya cewa komai akai 🤖🤝❤️
By khalifa Aminu
02/06/2026
Dangin Junaydi sun ɓace gaba ɗaya ba tare da wata alama ba a shekara ta 1980 a kasar Masar. Wannan iyali na daga cikin shahararrun iyalai kuma mafiya kuɗi a wancan lokaci.
Amma yadda s**a ɓace, abin da ya same su, da dalilin da yasa aka rufe shari’arsu akan wanda ba a sani ba, duk waɗannan s**a zama tambayoyi babu mai amsawa.
Har yanzu duk wata shaida tana nuna cewa gidan Junaydi cike yake da ruhohin da s**a fusata. Mutane suna guje masa, har ma maƙwabta sun sayar da gidajensu saboda tsoron muryoyin da suke ji daga gidan.
Ni kaina tun ina ƙarama a titn Dawud Basha, ɗan uwana yakan gargade ni kada in kuskura in shiga wannan t**in, musamman bayan ƙarfe bakwai na yamma. Kuma saboda ni, na fi kowa karanta labarai game da wannan iyali da abin da ya same su.
Yawancin marubuta sun yi amfani da labarinsu wajen ƙirƙirar tatsuniyoyi, amma babu wanda ya iya faɗar gaskiyar abin da ya faru. Kamar sirrin da aka boye tare da su…!
Farkon Abin Da Ya Faru
Wata rana ina wajan bikin abokiyata. Lokaci ya ja har ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare, alhali har yanzu tafiyar fiye da awa guda take tsakanin ni da gida.
Na kira ɗan uwana domin ya zo ya ɗauke ni, amma ya ce yana aiki da dare, ba zai iya ba. Ya ce in kira Uber, shi ne mafi sauri.
Na yi hakan cikin gaggawa, saboda ban son mahaifina ya yi fushi saboda na makara.
Motar Uber ta iso, na shiga cikin hanzari har ban ma kula da fuskar direban ba. Duk abin da nake faɗa masa shi ne:
Don Allah, ka yi sauri… lokaci yana tafiya.
Mun isa Masar Jadida da sauri. Na fara jin sauƙi, amma sai motar ta shiga cikin t**in Dawud Basha!
Na firgita:
“A’a! Kada ka shiga nan, don Allah! Ka wuce da t**in gaba.”
Amma direban bai saurare ni ba.
Na ce cikin rawar murya:
“Ya ustaz, ka dawo baya! Wannan t**in haɗari ne.”
Da na dubi fuskar sa sosai, sai na ga ya na sanye da kufiyya. Fuskar sa a rufe take!
Zuciyata ta fara bugawa da ƙarfi. Na yi ƙoƙarin buɗe ƙofar mota a hankali, amma sai na gano duk ƙofofin a kulle suke! Kamar dai an yi niyyar sace ni!
Na ce da shi cikin tashin hankali:
Me yasa baka magana? Ka sauke ni anan! Zan kai rahotunka ga Uber, duk bayananka suna nan.”
Amma bai motsa ba, k**ar gunki.
Sai kawai na yi shiru, ina jiran abin da zai faru. Motar ta tsaya tsakiyar t**i, dai dai gaban gidan Dangin Junaydi!
Ganin Abin Da Bai Kamata Ba
Na san gidan tun ƙuruciya, duk da cewa ban taɓa kusantar sa haka ba.
A nan ne direban ya yi magana karon farko:
Sauka…
Muryarsa ta ban mamaki, ba muryar namiji ba bace ba, muryar yaro ƙarami ne!
Na kalle shi da firgici… a wani yanayi kuma ya ɓace daga cikin motar!
Na sauka ina rawar jiki, zufa ta hadu sosai a jikina da barin jiki da faduwar gaba,
Na tsaya ina kallo, t**i babu kowa, babu wata murya, sai ƙamshin kura da ɗanɗanon datti,
Gidan ya tsaya gabana, k**ar yadda na saba gani daga nesa: tagogi a fashe, ƙofofi a rufe. Amma abin da ya sa na yi ihu shi ne: dukkan fitilu a cikin gidan s**a haskaka a lokaci guda!
Ba wutar lantarki ba, sai wani haske mai rawaya k**ar fitilar kyandirori da yawa.
Na tsaya cak, sannan na ji muryoyi da dama suna raɗa:
“Kin dawo… ehhh… kin dawo.
Na firgita: dawo? Ni ban taɓa zuwa nan ba!
A nan ne ƙofar gidan ta buɗe da ƙarar ƙara mai ban tsoro.
Na hango su… Dangin Junaydi!
Dukansu suna tsaye ciki, k**ar an tsayar da su a cikin lokaci:
Kakansu yana zaune akan kujerar katako.
Tsohuwa a tsaye cikin doguwar riga baƙa.
Yara suna kewaye da su cikin tsoffin kayan daga shekarun 70’s.
Idonsu duk baki ne, babu farin ciki a cikinsu.
Sai muryar wancan yaro ta dawo, muryar da ta fito daga direban:
“Ke ɗin tawa ce… yaya kika manta dani?”
Na yi ihu:
>“Ban da alaƙa da ku ba! Don Allah Ku bar ni!”
Sirrin da Aka ɓoye
Sai na ji hannun yaro ya k**a rigata daga baya. Na juyo da sauri, sai na ga ƙaramin yaro da gashinsa a hargitse,
Ya ce:
Dukkanmu an ɓatar da mu anan… wanda ya shiga ba ya fita. Ke ce kawai za ki iya bayyana gaskiya.”
Na ce da tsoro:
“Wacce gaskiya?”
Ya yi kuka yana ce wa:
An kashe mu duka… aka ɓoye gaskiyar. Kuma wanda ya kashe mu yana raye har yanzu. Sunan sa Khalid Khalil Amma mutane sun yi shiru. Ki taimaka mu, in ba haka ba za ki kasance da mu har abada anan.
Muryoyin s**a ƙaru, gidan ya fara karkarwa, ihu yana ƙara tashi.
Na fara juyawa, zuciyata na neman tsayawa. Sai na ji wani abu ya rufe ni, kuma na suma.
Ƙarshe
Na farka a tsakar t**i, a waje da gidan. Motar ta ɓace, rayuwa ta koma daidai, mutane suna tafiya k**ar babu abin da ya faru.
Amma tun daga wannan rana, duk lokacin da na wuce wajen gidan Junaydi, sai na ji wata ƙaramar murya tana raɗa a kunnena:
Kada ki manta… bayyana gaskiya yana tare da ke.
Yanzu ina tunanin ta ina zan fara....... Domin bayyana gaskiya
Idan kana son labarai da karatu, kalaman hikima, nishadi, ilimantarwa,gamida labaran tarihi da abubuwan al'ajabi,kai following AWAINIYA.com
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Website
Address
Abuja