Manara RADIO

Manara RADIO

Share

09/06/2026

LABARUN DUNIYA

GWAMNATIN OYO TA RUGUJE GIDAN BOYE WADANDA A KA SACE A BADUN

Gwamnatin jihar Oyo a kudu maso yammacin Najeriya ta ruguje wani gida da barayin mutane ke adana wadanda su ka sace a babban birnin jihar Badun.
Wannan ya biyo bayan gano 'yar uwar tsohon ministar lantarki Adelabu da barayin su ka sace ranar 3 ga watan nan su ka ajiye su a gidan.
Akasin ya faro ne da sace Busayo John Paul a lokacin da ta ke kai 'ya'yanta tagwaye Peter da Paul makaranta a nan Badun din.
Ruguje ginin ya zo 'yan sa'o'i bayan kwamishinan 'yan sanda na jihar CP Abimbola Olugbenga ya zaga da manema labaru don duba ginin.
Kwamishina Olugbenga ya ce akwai mamaki yadda gidan da ke tsakiyar jama’a kuma mutane na ganin wadanda a ke satowa a kawo amma ba tare da kai rahoto ga hukuma ba.
Wadanda a ka sacen na cewa su na jin hada-hadar makwabtan gidan amma ba su iya fitowa ba.
Olugbenga ya bukaci jama’a su rika kai rahoton satar mutane ko wasu laifuka don daukar matakan da su ka dace.

GHANA TA DAWO DA 'YAN KASARTA 1000 DAGA AFURKA TA KUDU

Kasar Ghana ta yi nasarar dauko 'yan kasarta kimanin 1000 daga Afurka ta kudu inda a ke fama da kin jinin baki.
'Yan Afurka bakar fata na fama da hare-hare daga 'yan Afurka ta kudu kuma har hakan kan yi sanadiyyar mutuwa ko kisan gilla da asarar dukiya.
Ministan harkokin wajen Ghana Samuel Ablakwa ya fitar da sanarwar dawo da mutanen zuwa gida don kare su daga fitinar Afurka ta kudu.
An tanadi tsari na maraba da wadanda a ka dawo da su ta hanyar alkawuran sama mu su aiki kuma an raba mu su layukan waya da damar hawa yanar gizo don samun sadarwa da dangi da sauran abokan hulda.
Mutanen sun yabawa shugaban Ghana John Dramani Mahama don daukin da ya yi mu su.
Najeriya ma ta dau matakai ciki har da magana da hukumomin Afurka ta kudu su hukunta masu hannu wajen hare-haren kin jinin baki don ya zama matakin dakile mummunar dabi’ar.

ISRA’ILA DA IRAN SUN SHIGA SABON DAUKI BA DADI

Isra'ila da Iran sun shiga sabon dauki ba dadi da juna da hakan ke barazana ga wanzuwar shirin tsagaita wuta na Amurka.
Hare-hare da Isra’ila ke kai wa kan Lebanon da zummar gamawa da duk 'yan Hezbollah da Iran ke marawa baya ya haddasa daukar matakai daga Iran din.
An yi musayar hare-hare tsakanin kasashen biyu kuma an ga wajejen da Isra'ila ta kai wa farmaki a Tehran, Tabriz da Isfahan
Iran na bukatar a shigar da Lebanon a cikin yarjejeniyar tsagaita wuta ta na mai zargin Amurka da Isra’ila da keta yarjejeniyar.
Ba ma abun da ya fi zama damuwa irin hare-hare kan yankin Dahiyeh na kudancin Lebanon da kuma sassan tasoshin ruwa na Iran.
A nan alamu na nuna sai an samu jajircewa daga mai shiga tsakani wato Pakistan don wanzar da yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran.

SAUDIYYA MUSANTA HARI KAN FILIN JIRGIN SAMA NA YARIMA SULTAN

Saudiyya ta musanta wani rahoton hari kan filin jiragen sama na Yarima Sultan bin Abdul'aziz a yankin Alkharj.
Kakakin rundunar sojan Saudiyya Janar Turki Almaliki ya ce bayanan kai harin ba gaskiya ba ne.
An dai kunna jiniyar ankarar da mutane yiwuwar hatsari don harbo makami da a ka yi daga cikin Yaman amma makamin ya tsaya a hanya kuma harin bai yiwu yadda a ka tsara ba.
Hakika an daina samun hare-hare daga 'yan houthi a Yaman zuwa Saudiyya tun sulhun da a ka samu tsakanin Saudiyya da Iran zamanin shugabacin marigayi shugaban Iran Ebrahim Raisi da marigayi ministan wajen Iran Amir Hossein Abdollahian ya yi ta kai kawo har a ka dawo da dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.
Kasar Sin ta taka rawa wajen sulhunta Iran da Saudiyya amma hare-hare na Amurka da Isra'ila kan Iran sun sa mayar da hannun agogo baya.

04/06/2026

LABARUN DUNIYA

MAJALISAR DATTAWA ZA TA DUBA MAFITA GA ‘YAN MAJALISAR 40 DA BA SU SAMU TIKITIN ZABE BA

Majalisar dattawan Najeriya ta bayyana aniyar duba mafita ga ‘yan majalisar 40 da ba su samu tikitin tsayawa zabe a zaben 2027 da ke tafe ba.

Shugaban majalisar Godswill Akpabio ya bayyana haka ga wadanda lamarin ya shafa kuma su ke cikin yanayin jiran tsammanin samun wata mafita bayan gudanar da zabukan fidda gwani a jihohinsu da wasu ke zargin gwamnoni sun yi babakere.

A wani lokaci a baya k**ar ‘yan majalisar sun samu albishir na cewa duk za su zarce in an zo babban zabe amma sai 40 a cikinsu su ka rasa damar.

‘Yan majalisar 40 da akasari daga jam’iyyar APC ne na cikin ‘yan majalisa 109 na majalisar dattawan.

Ba shakka an samu irin wannan bita ga wasu fitattu a majalisar a baya da su ka hada da shi kansa shugaban majalisar Godswill Akpabio da tsohon shugaban majalisar Ahmed Lawal.

Ba mamaki maslahar ta iya fitowa ta hanyar jam’iyya ko tattaunawa da gwamnonin da kuma yiwuwar tafiya kotu.

A na raderadin shugaba Tinubu ka iya sa baki ga wasu ‘yan jam’iyyar APC duba da irin gudummawar da su ka bayar ta goyon baya a majalisar ta 10.



BABBAR KOTUN TARAYYA TA YANKE HUKLUNCIN KISA GA WADANDA KE DA HANNU A HARIN OWO

Babbar kotun tarayyar Najeriya a Abuja ta yanke hukuncin kisa ga mutum 4 da ta samu da hannu a harin ta’addanci kan majami’ar katolika ta Owo a jihar Ondo a shekara ta 2022.

Harin dai na ta’addanci ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 41 da kuma raunata wasu mutum 140.

Mai shari’a Jostis Emeka Nwite ya yanke hukuncin bayan shari’ar da ta dau tsawon wata 8 kuma kisan zai gudana ta hanyar rataya.

Wadanda a ke samu da laifin an tabbatar na cikin kungiyar ta’addancin Alshabab da ke aiki a wajajen Kwara da Ondo.

Mutanen sun hada da Idris Abdulmalik Omeiza mai shekaru 25, Alqasim Idris mai shekaru 20, Jamiu Abdulmalik mai shekaru 26 sai Abdulhaleem Idris mai shekaru 25.

Duk da haka kotun ba ta samu mutum na cikon biyar mai suna Momoh Oyubo Abubakar mai shekaru 47 da laifi ba don haka ta wanke da sake shi.



JAM’IYYU 15 SUN SAMU MIKA SUNAYEN ‘YAN TAKARARSU GA INEC BISA KA’IDA

Jam’iyyu 15 sun samu nasarar mika sunayen ‘yan takararsu ga zaben shugaban Najeriya na 2027 kanm ka’idar lokacin da hukumar zabe ta gidaya wato zuwa 30 ga watan jiya.

Duk da an samu wani hukuncin kotu da ke buda damar har watan Satumba, amma jam’iyyu 15 sun samu nasarar mika sunayen da su ka hada da sanannu da kuma wadanda ba a saba jin sunayensu ba.

‘Yan takarar sun hada da na jam’iyyar da ke gado APC wato shugaba Bola Tinubu, sai a adawa ADC ta tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayin da sabuwar jam’iyyar adawa ta NDC ta tsayar da Peter Obi.

Wata takarar mai daukar hankali ita ce ta tsohon shugaba Goodluck Jonathan a PDP duk da an samu dan takarar bangare sai kuma Donald Duke a jam’iyyar PRP ta Malam Aminu Kano.



ISRA’ILA DA LEBANON SUN CIMMA WATA YARJEJENIYAR DAKATAR DA HARE-HARE

Isra’ila da Lebanon sun cimma yarjejeniyar dakatar da hare-hare biyo bayan zama karo na 4 da shiga tsakani na Amurka.

A nan sabuwar yarjejeniyar ta nuna Hezbollah za ta janye daga dukkan sassan kudancin Kogin Litani da ke dumfarar kan iyakar Isra’ila.

Kazalika a sassan tsaro na yankin an cimma amincewar sojojin gwamnatin Lebanon za su karbi dukkan matakan tsaro yayin da Hezbollah ta janye gaba daya.

Ba shakka dakatar da musayar wuta tsakanin Isra’ila da Hezbollah na daga sharuddan tsagaita wuta a yakin Iran da Amurka inda Iran ta ce lallai sai Isra’ila ta daina kai hare-hare kan Hezbollah in ba haka ba ba yarjejeniya tsakaninta da Amurka da ma Isra’ila.

Iran dai ke marawa Hezbollah baya inda ita kuma kungiyar ta Hezbollah ke tinkarar Isra’ila don hanata sakat matukar za ta cigaba da hare-hare kan Iran ko yankin Gaza.

02/06/2026

LABARUN DUNIYA

SHUGABA TINUBU YA JINJINAWA RUNDUNAR SOJAN RUWA YAYIN DA TA KE CIKA SHEKARA 70 DA KAFUWA

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jinjinawa rundunar sojan ruwan Najeriya don aiki tukuru a yayin da ta ke bukin shekara 70 da kafuwa.

Wannan ya faru a taro da a ka gudanar a mashigar bakin ruwa ta EKO ATLANTIC a birnin Lagos.

Shugaban ya kuma kaddamar da jiragen ruwa uku don inganta ayyukan rundunar da su ka hada da NNS Olobiri, NNS Mambila da NNS Gurara.

Shugaba Tinubu ya ce hakika rundunar sojan ruwan Najeriya ta taka rawa wajen yaki da barayin man fetur na teku da ya ce hakan ya kara bunkasa hako danyen man fetur.

Kazalika shugaban ya ce rundunar ta yi kwazo wajen yaki da ta’addanci da ma yin su ba tare da izini ba.

Da ya ke jawabi shugaban rundunar sojan rowan Vice Admiral Idi Abbas ya ce sun samu nasarori a ‘yan shekarun nan da kulawar shugaban ga rundunar.

Idi Abbas ya yi amfani da damar wajen nanata mubaya’ar rundunar ga kundin tsarin mulki da kuma shuagban kasa.



‘YAN BINDIGA SUN YI KISAN GILLA GA KIMANIN MUTUM 8 A JIHAR FILATO

‘Yan bindiga sun yi kisan gilla ga kimanin mutum 8 da raunata wasu mutum 10 a yankin Barikin Ladi da ke jihar Filato.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun shigo yankin su na harbin kan mai uwa da wabi inda hakan ya tilasta mutane su ka arce don samun mafaka.

Mutanen dai da a ka kai wa hari na gudanar da taron murnar zagayowar ranar haihuwa ne BIRTH DAY a lokacin da maharan su ka shigo.

Kungiyar kare hakkin Dan’Adam ta AMNESTY ta yi Allah wadai da kisan gillar ta na mai dora alhakin hakan kan hukuma da matakanta ba su wadatar wajen kare rayukan jama’a ba.

Ba bakon abu ba ne samun hare-hare a jihar Filato da kan sa mutane zullumin samun harin ramuwar gayya ko ma aukawa fadan kabilanci ko ma na bambancin addini.



NDLEA TA CE MASU SHAN MIYAGUN KWAYOYI YANZU HAR DAFIN MACIJI SU KE AMFANI DA SHI

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta bayyana cewa yanzu mashaya miyagun kwayoyi sun kai ga amfani da dafin maciji don samun buguwa.

Daraktar wayar da kan jama’a na hukumar Shehu Muhammad Dankolo ya bayyana haka bayan kaddamar da gidan rediyo FM mai taken CLEAN BEAT na hukumar a Abuja.

Shehu Dankolo ya bayyana cewa masu shan miyagun kwayoyin kan yi dabarar aiki da abubuwan da ba sa cikin doka don samun maye k**ar dafin maciji, kashin kadangare, bunne bawali ya kwan biyu da sauran hanyoyi don kaucewa doka.

A nan Dankolo ya bukaci tsaurara dokokin hukunta masu shan miyagun kwayoyi don hakan zai taimaka wajen yaki da kwayoyin da kan haukata musamman matasa.

Dankolo ya ba da shawarar daina korar jami’an tsaro da a ka samu da aikata laifuka sanadiyyar shan miyagun kwayoyi don kar su kara tsunduma miyagun laifuka; kuma maimakon hakan a tura su cibiyoyin NDLEA na sauya tarbiyya don daidaita dabi’arsu.



TRUMP YA CE HAR YANZU AMURKA NA TATTAUNAWA DA IRAN DON SAMUN SULHU

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce har yanzu kasarsa na zantawa sosai da Iran don samun sulhun tsagaita yaki a yayin da Iran ta bayyana janyewa da duk wata yarjejeniya biyo bayan kutsawa can cikin Lebanon da Isra’ila ta yi.

Trump ya ce Iran ba ta sanar da Amurka cewa ta janye daga tattaunawa ba don haka duk tsawon lokacin tsagaita tattaunawar ba zai hana cimma buri ba.

Donald Trump ya ce a yi shiru ma a jira ya fi alheri don samun cimma yarjejeniyya, amma shirun ba ya nuna Amurka za ta kai farmaki kan Iran.

Duk da haka Trump ya ce kange tasoshin jiragen ruwa na Iran da Amurka ta yi na nan.

Iran dai ta nuna matukar takaici ga yadda Isra’ila ke aukawa Lebanon da sunan murkushe Hezbollah da hakan kan yi sanadiyyar kashe rayukan fararen hula da asarar dukiya.

Want your business to be the top-listed Media Company in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address


Utako District
Abuja