Ibn Taheer
13/12/2025
TARON CIKA SHEKARA 10 DA WAKI'AR BUHARI A ZARIYA A ABUJA
Harkar Musulunci karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), ta fara gudanar da taron tunawa da waki'ar Buhari a Zaria, waki'ar da Buhari yayi umarnin su Burtai s**ayi kwanaki uku suna kisan kiyashi a Husainiyya Bakiyatullah, da gidan Jagora (H) dake Gyallesu, da Darur-Rahma dake cikin garin Zariya ta Jahar Kaduna.
An fara gudanar da taron da addu'a, daga bisani aka gudanar da gagarumin majalisul aza, sannan aka fara sauraren bayani daga wanda akayi waki'ar Buhari a idonsu, Malam Isma'il D Usman, shine ya fara bayani akan yadda waki'ar Buhari ta ritsa dasu a Husainiyya, sai Ammah Habiba Zariya" ita kuma tayi bayani ne akan yadda 'ya'yanta s**ayi shahada da Mijinta. Daga karshe Sheikh Muhammad Abbari wakilin yan'uwa na garin Gombe ya gabatar da jawabi maudu'i mai taken (Shekaru Goma da waki'ar Buhari, sadaukarwa a tafarkin Allah, darussa daga waki'ar Buhari), sannan aka rufe taro da addu'a aka sallahmi jama'a.
Jiya Juma'a shine ya zama rana ta farko cikin jerin ranakun da za'a gudanar da Taron a Abuja, za'a cigaba da taro gobe, idan Allah ya kaimu
'arBuhariShekara10
12th/ Dec/ 2025
06/12/2025
GAYYATA ZUWA TARON CIKA SHEKARA 10 DA WAQI'AR BUHARI
Harkar Musulumci karkakashin jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky (H)
Na sanar da daukacin al'ummar gaba daya cewa, za ta gudanar da taron tunawa da waqi'ar Buhari shekara (10) goma kamar yadda ta Saba gudanarwa duk shekara tun bayan waqi'ar.
Wannan gagarumin taron zai gudana ne na tsawon kwanaki uku kamar yadda aka saba.
Jadawalin taron zai kasance Insha Allah kamar haka:-
Rana ta daya :- Juma'a 12th December, 2025 dai-dai da 21st Rabi'ul Thani, 1447
Abinda za'a gudanar
Jawabai dangane da waqi'ar Buhari da Wakokin tunawa da waqi'a din.
Rana ta biyu :- Asabar, 13th December, 2025 dai-dai da 22nd Rabi'ul Thani, 1447
Abubuwan da za'a gudanar
Conference da exhibition
Masana a bangarori da dama za su gudanar da jawabai.
Rana ta uku :- Lahadi, 14th December, 2025 dai-dai da 23rd Jumada Thani, 1447
Abubuwan da za'a gudanar
Jawabai daga bakin iyalan Shuhada, Wadanda waqi'ar ta shafa da kuma Wakokin tunawa da waqi'ar Buhari shekara 10.
Allah ya bada ikon halarta.
Sanarwa daga.
Mu'assasatu Abul-Fadl Abbas, Academic da sisters forum
Basu taba karaya ko mika wuya domin ba'a san rundunar Allah da tsoro ba
12 🅳🅴🅲🅴🅼🅱🅴🆁 2015.
Hira da wasu Iyalan Shahidai da 𝗕𝘂𝗵𝗮𝗿𝗶 ya kashe wa 𝗶𝘆𝗮𝘆𝗲 a waki'ar ta 𝗕𝘂𝗵𝗮𝗿𝗶.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Abuja