Ya-Ibadeeh

Ya-Ibadeeh

Share

11/03/2025

____________
*SADQATUJJARIYA*
Ku saka taro ko sisi Ciyarwa ga mabukata tare da cibiyar *YA-IBADEEH & ELFARI FOUNDATION*
Musamman a wannan lokaci
*ASUSUN TALLAFI* ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ
1-Acc. No. 6117395590
Name:- Fari Hamisu
Opay
2-Acc. No. 1000000007
Name:- Fari Hamisu
Tenn bank.
_______________________
Atayamu isar da saฦ™o ta hanyar turawa sauran zaurukan.
________________________
Facebook ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ
https://www.facebook.com/profile.php?id=100065016631053
Community ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ
https://chat.whatsapp.com/ISjoy10h9vF1bxM3LQWEJY
_____________________
*ยป๐Ÿ‘‰๐Ÿผ YA-IBADEEH COMMUNITY*๐Ÿ“–๐Ÿ•‹

Ya-Ibadeeh Library

12/02/2023

*_HUKUNCIN FADIN (JUMA'AT MUBARAK)_*

*Tambaya*
Assalamu Alaikum. Dr ko ya halatta Musulmi yayi wa dan'uwansa murna da zagayowar juma'a ta hanyar sako a wayar sailula k**ar ace JUMA'A KAREEM ko JUMA'A MUBARAK? Allah yaqara sani.

*Amsa:*
Wa'alaikum assalam, Akwai malaman da su ka hana hakan, suna ganin ba shi da asali a addini, Amma abin da yake zahiri hakan ya fi k**a da al'ada, wannan yasa haramta shi yake bukatar Nassi, tun da babin al'adu da mu'amaloli a bude yake, sai abin da sharia ta haramta. Duk Wanda yake yi ba tare da ya riya cewa ibada ba ce hana shi ko bidi'antar da aikinsa yana da wuya, k**ar yadda Ibnu Uthaimin ya yi nuni zuwa haka a fatawar da aka yi masa.

Saidai duk da haka ya k**ata kar Musulmi ya zamar da shi al-adarsa kowace juma'a, don kar wasu su fahimci ibada ne.

Allah ne mafi sani.
____________________
*Amsawa;- Dr Jamilu Zarewa*
____________________
Ku kasance damu a๐Ÿ‘‡๐Ÿผ
Facebook ๐Ÿ‘‰๐Ÿผ https://mobile.facebook.com/Ya-Ibadeeh-105630640871237
_____________________
*ยป๐Ÿ‘‰๐ŸผDAGA ZAUREN YA- IBADEEH*๐Ÿ“–

mobile.facebook.com

10/02/2023

*TA KI YARDA DA MIJINTA SABODA TANA AZUMIN NAFILA?*

'''Tambaya:'''

_ AssalamuAlaikum, Malam ina da tambaya? Yaya,hukuncin Matar da miji ya bukaceta sannan tana Azumin sunna, taki ta Amince mishi. _

'''Amsa:'''

_ Wa alaikum assalam, ta yi kuskure ya k**ata ta amsa,kiran mijinta, saboda azumin sunna ya halatta a karya shi ko da babu dalili, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: * โ€œMai azumin nafila sarkin kansa ne ina ya ga dama ya cigaba da azumin, in kuma ya so yakaryaโ€ *.k**ar yadda Tirmizi ya rawaito a Sunan. _

Amma ya dace ta dinga shawartar mijinta aduk lokacin da zatayi Azumin nafila din domin samun sahalawa da daidaita al'amurra.

*Allah ne mafi sani*

_ *โœ๐ŸผDr Jamilu Zarewa *_
________________________
*Za'a iya bibiyar darussan mu a๐Ÿ‘‡๐Ÿผ*

Facebook๐Ÿ‘‰๐Ÿผ https://mobile.facebook.com/Ya-Ibadeeh-105630640871237.
_____________________
*ยป๐Ÿ‘‰๐ŸผDAGA ZAUREN YA- IBADEEH*๐Ÿ“–๐Ÿ•‹

mobile.facebook.com

Want your organization to be the top-listed Government Service in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


No. 7 Yahya Madaki Way Katsina
Abuja