Dr Rajj Abubakar
10/05/2023
BAYANI A KAN CUTAR CIWON HANTA (HEPATITIS) DA YADDA ZA A MAGANCE SHI💊🍵 DA IKON ALLAH☝🏻
Rubutawa; DR RAJJ ABUBAKAR ✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
☎️08103373096☎️
Ciwon Hanta (Hepatitis) : Kamar yadda kowa yasani Hepatitis cutar hanta ce wacce take kunburar da hanta, kuma kwayar cutar virus ce take kawoshi .
A mafi yawan lokuta wadannan kwayoyin cutar virus suna zamansu ne kawai a cikin hanta ba sa kawo wata illa, sai dai ta Hepatitis B za ta iya kawo ciwon cancer.
HEPATITIS Ya kasu rukuni daban daban :
1- Hepatitis A
2- Hepatitis B
3- Hepatitis C
4- Hepatitis D
5- Hepatitis E
Wacce tafi addabar mutane a kasarmu Najeriya🇳🇬 ?
Hepatitis B tafi addabar mutane a najeriya k**ar yadda bincike🔍🔎 ya nuna .
Tayaya Mutun Zai Dauki wannan kwayar cutar Hepatitis B ?
Awai Hanyoyi da dama ta yadda mutun zai iya daukan wannan cutar Hepatitis B . Ga kadan daga ciki :
1- Ana iya daukanshi ta hanyar jima'i (S*x) da mai dauke da cutar .
2- Yaro zai iya dauka daga uwa🤱🏻 lokocin haihuwa .
3- Ana iya daukanshi lokocin karin Jini🩸💉
4- Ana iya Daukanshi daga kayan kaifi k**ar su razor .
5- Ana lya daukan wannan cutan wajen amfani da syringe💉 guda daya zuwa mutane diyawa .
6- Ana iya daukan hepatitis ta hanyar abinci🍝 ko abin sha🍷🥃 wacce ta kurba ta da kashin mai dauke wannan cutar.
7- Ana iya daukan hepatitis ta hanyar kissing👩❤️💋👨 ko musayar yawu.
Ance kwayar cutar Hepatitis B mutun zai iya daukanshi lokocin Gaisuwa🤝🏻 ( shaking Hands )
Hmm Mutane suna fadan hakane dan sabida kwayar cutar Hepatitis B tana zama a Gumi , Yawu👅 , Fitsari , Hawaye😭 da Kashi kuma . shikenan suna nufin idan ka gaisa da mutun gumunku ya hadu kadauki Hepatitis B . to Bahaka bane👎🏻 .
Menene Halamomin Cutar Hepatitis B ??
Wani lokoci ana samun mutum mai dauke da wannan kwayar cutar ba tareda ta nuna halama ba.
Amma ka kadan cikin halamominta :
1- Rashin cin abinci
2- Tashin zuciya💔
3- Amai😲
4- Rashin Karfin Jiki
5- Hajijiya 🤦🏻♂️🤦🏻♀️
6- Ciwon Ciki
7- Ciwon Gabobi
8- Canxa kalar fata zuwa yellow
9- Canxa kalar ido zuwa yellow 👁️👁️
10- wani lokocin da Zazzabi .
11- Bakin fitsari.
12- Kaikayin Jiki.
13- Canza launin bahaya zuwa kore.
14- Kasala.
Amma idan kaga mutun yana fama da wadannan halamomin ba shi zai tabbatar maka da cewa yana dauke da kwayar cutar Hepatitis B ba . sai an je asibiti🏥 an gwada👨🏻⚕️ an tabbata .
KARIYA DAGA CUTAR HEPATITIS B:
1- Hepatitis B tana da vaccine wanda a kalla mutum zai dauka so uku zuwa hudu kafin yasamu kariya.
Yara kanana ana basu k**ar haka:
1- at 0 (dabane haifi yaro)
2- at 6wks ( Buti shidda da yin na farko)
3- at 10weeks ( bayan sati hudu da yin na biyu)
4- at 14weeks ( bayan sati hudu da yin na uku).
Shine wannan alluran zai yiwa babba amfani naga yara ake bawa a asibity?
Eh zaiyiwa manya amfani dalilin da yasa yara kadai ake bawa shine wadanda s**a dauki nauyin kawo wannan vaccines din target age nasu yara kanana ne👶🏻👶🏻 sabida sunfi hatsarin kamuwa da cutar.
2- Dukkanin abinda muka lissafa zai kawo wannan cutar a kiyaye shi a kula.
Idan mutum ya tabbatar yanada wannan cutar me yak**ata yayi ?
Abinda yak**ata yayi shine yaje aisbiti🏥 ya tabbatar Kuma a daura shi kan magani👨🏻⚕️💊
Wanne Erin abinci mai wannan matsalar hepatitis zaiyi amfani da shi ?
Tunda wannan cutar tana k**a hanta yak**ata a dauki matakan da zai karawa hanta lafiya da karfi ta hanyar excercise da abinci masu inganci k**ar su :
1- Kayan itatuwa - tana dauke da sinadaran vitamin, fractus da fiber wanda zai karawa hanta lafiya kuma yakan yaki cututtuka.
2- Protein : dangin abinci mai dauke da sinadaran gina jiki ( k**ar su kifi , kaza banda fatar sama da wake) s**an gyera cell na jikin Dan Dama wanda hakan zai karawa hanta lafiya.
3- Abinci dangin hatsi irinsu gyero, dawa shinkafa suma basu da matsala mutum zai iya amfani da su.
4- Mutum zai iya amfani da man zaitun da habbatus sauda basa daga cikin man da suke kawo illa amma suna yakan cututtuka.
5- Motsa jiki🏃🏻♀️🏃🏻♂️ cikin Dan Adam ayana bukatar motsa jiki hakan zai karawa jiki lafiya.
Note:
Lokocin cin abinci a raba ciki zuwa gida uku:
09/05/2023
MAGANIN DA YAKE CHIKO DA NAMAN FARJIN MACE TAREDA KARA NI'IMA
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
DAKWA ROAD NEW SAYE Plaza OPPOSITE POLICE STATION. , OFFICE NO A-14
Abuja
Opening Hours
| Monday | 09:00 - 23:00 |
| Tuesday | 09:00 - 23:00 |
| Wednesday | 09:00 - 23:00 |
| Thursday | 09:00 - 23:00 |
| Friday | 09:00 - 23:00 |
| Saturday | 09:00 - 23:00 |
| Sunday | 09:00 - 23:00 |