Hausa Light

Hausa Light

Share

Photos from Hausa Light's post 05/12/2023

JIBWIS tayi Allah wadai ta kisan gungun musulmai a kaduna

Kungiyar wa’azin musulunci ta Izala tayi Allah wadai da kisan kiyashi na harin wani jirgin sama da aka yiwa al’ummar musulmai a jahar kaduna yayin da suke gudanar da wani taro.

Shugaban kungiyar Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga gwamnantin tarayya da tayi bincike na gaskiya Akan hakikanin abun da ya faru, kuma ta hukunta masu hannu a cikin wannan lamari.

Lamarin de ya faru ne a kauyen Tudun Biri da ke gundumar Afaka a lardin Rigasa a karamar hukumar Igabi, inda aka yi kuskuren kashe musulman da suke gudanar da wani taro tare da jikkata wasu da dama biyo bayan wani hari da jirgin yaki mara matuki na soja ya kai don farautan ‘yan ta’ada.

Sheikh Bala Lau yayi jimami kwarai, ganin yadda daruruwan mutane s**a rasa ransu a wannan lamari. A karshe yayi addu’ar Allah ya Jikan musulmai muminai, ya baiwa wadanda s**a ji rauni lafiya, ya kuma kiyaye faruwar haka a gaba.

JIBWIS NIGERIA

Photos from Hausa Light's post 29/11/2023

Ana zargin mazauna Unguwar Kurna sun rufe titin Kurna Rijiyar Lemo ba shiga ba fita, bisa zargin wani Dan sanda da harbin wani matashi, da wasu mutane biyu, ƙarin bayani na nan tafe.

Freedom Radio Nigeria

Photos from Hausa Light's post 29/11/2023

BABBAN LABARI

Masarautar Katsina ta Sallami Magajin garin Funtua Alh Rabiu Aliyu Nuhu, Sanarwar na zuwa ne a wata takarda da masarautar ta fitar ranar litinin 27-11-2023 Mai dauke da Sanya hannun Sarkin yakin katsina Alh Bello M. IFO.

Funtua Online Tv.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Abuja