Pharmactivity

Pharmactivity

Share

06/04/2026

Kwanan baya nayi magana akan allurar GENTAMICIN INJECTION yau kuma ga wayar da kan al’umma, musamman masu kananan shagunan magani (chemist), game da amfani da GENTAMICIN EYE DROPS a idanu.

A mafi yawan lokuta, idan mara lafiya ya je chemist ya nemi maganin ciwon ido, abin da ake yawan ba shi kai tsaye shi ne Gentamicin eye drop, ba tare da an tantance irin ciwon idon ba.

Abin da mutane da yawa ba su sani ba shi ne: Gentamicin antibiotic ne— wato magani da ake amfani da shi wajen kashe kwayoyin cutar bacteria. Amma ba dukkan ciwon ido bacteria ke haifarwa ba.

Idan aka yi amfani da shi alhali ba bacteria ce ke haddasa ciwon idon ba, akwai matsaloli guda biyu:

1. Zai iya haifar da resistance (wato kwayoyin cuta su saba da maganin har ya daina aiki nan gaba)
2. Kuma mutum ya bata kudinsa a banza ba tare da samun waraka ba

Ciwon ido iri-iri ne:
1. Akwai wanda bacteria ke haifarwa
2. Akwai wanda virus ke haifarwa
3. Akwai kuma wanda ba kwayoyin cuta ba ne ke jawo shi (kamar allergy ko bushewar ido) Kowanne daga cikin wadannan yana da alamomi daban-daban, kuma maganinsu ma ya bambanta.

Wani lokaci, abin da mutum ke bukata ba antibiotic ba ne, sai dai:

A. Maganin rage kaikayi
B. Ko maganin da zai sa ido ya samu danshi (lubricating eye drops)

Na sha samun marasa lafiya da s**a ce sun yi amfani da maganin ciwon ido har ya kare amma basu samu sauki ba. Idan aka bincika, sai a ga sun yi amfani da Gentamicin, alhali ba shi ya dace da matsalarsu ba.

Saboda haka, yana da matukar muhimmanci a tantance irin ciwon ido kafin a ba da magani.

Yanada kyau duk lokacin da ka ji ciwon ido, ka nemi shawarar kwararren ma’aikacin lafiya domin a baka shawara da ya dace, kuma a kauce wa amfani da magunguna ba tare da dalili ba.

Dr. Abdulhakam Usman
Clinical Pharmacist

📸: AI manipulated!

03/04/2026

Jama'a, ku rik'a shan ruwa sosai ak'alla leda 5-6 na pure water (2.5-3 litres) a rana. Kudaina shan magunguna barka tai batare da k'aida ba. Ku ki yaye lafiyar kodar ku.

Photos from Pharmactivity's post 12/02/2026

ME YA KAMATA MUTUM YASANI DANGANE DA HAWAN JINI?

Want your business to be the top-listed Health & Beauty Business in Lucknow?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address


Lucknow
226026