Smartdata4u

Smartdata4u

Share

16/04/2026

I'm in the top 0% of Musti manzo fans. I earned 859 points on their weekly engagement list last week.

14/04/2026

ZUWA GA MAZINATA

Ya kai bawan Allah… ka tsaya ka yi tunani 🤲
Wannan abin da kake yi zina ba ƙaramin laifi ba ne a wajen Allah.
Allah Maɗaukaki ya ce a cikin Al‑Qur'an:
“Kada ku kusanci zina, domin ita alfasha ce kuma mummunan hanya.” (Suratul Isra’i: 32)

Ka sani:
Zina tana lalata zuciya da imani
Tana jawo fushin Allah
Tana rushe albarka a rayuwa
Tana jawo bala’i da nadama a duniya da Lahira
Manzon Allah ﷺ ya nuna cewa imani yana raguwa lokacin da mutum yake aikata irin wannan sabo.
Amma ga mafita: 👉 Ka tuba yanzu kafin lokaci ya kure maka. Ka yawaita istigfari. Ka nisanci duk abin da zai kai ka ga wannan sabo (kallo, hira, kadaici da mace/namiji). Ka nemi aure idan kana da hali.

kyawawan halaye su ne mafi girman abin da ke ɗaga darajar mutum a cikin al’umma.
Àllah ya kyauta.. Ka tuna: Allah Mai rahama ne. Duk girman zunubi, idan ka tuba da gaskiya Allah yana iya gafarta maka idan Yasoo.
Saƙo na ƙarshe gare ka: Kada ka bari sha’awa ta kai ka wuta 😢
Ka dawo ga Allah yau, domin ganin gobe bata tabbata ba.
Allah ya tsare mu daga zina, ya tsarkake zukatanmu 🤲

Want your business to be the top-listed Computer & Electronics Service in Dairah?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Dairah