Taskar dadylasting
21/01/2026
A wani ƙauye, akwai wani saurayi mai suna Sadiq, yana da ƙwazo amma bai da haƙuri. Duk abin da zai yi, sai da gaggawa.
Wata rana aka ba shi damar aiki tare da wani dattijo mai suna Malam Bello, wanda yake samun riba kaɗan-kaɗan amma kullum bai taɓa shiga matsala ba.
Sadiq ya raina dattijon yana cewa: “Ni ina son riba mai yawa cikin lokaci kaɗan.”
Sai ya shiga wani aiki da bai yi bincike ba, cikin sauri ya zuba duk jarinsa. Kwana biyu kacal sai komai ya lalace, ya rasa duk abin da yake da shi.
Da ya koma wurin Malam Bello cikin kunya, sai dattijon ya ce masa: “Ba sauri ke kai mutum ga nasara ba, hankali da haƙuri su ne ginshiƙi.”
Tun daga wannan rana, Sadiq ya canja halinsa, ya fara yin abu a hankali, yana tunani kafin yanke hukunci. A ƙarshe, sai ya fi inda yake a da.
Darasi:
Wanda ya yi haƙuri ya yi tunani kafin aiki, shi ne ke kai wa ga nasara ingantatce
16/01/2026
Wani matashi yana aiki a kasuwa yana sayar da kayan hannu. Kullum idan aka tambaye shi farashi, sai ya ce: “Duk dai ɗaya ne, ka biya abin da ka ga dama.”
Saboda haka mutane suna ɗaukar kaya su ba shi kuɗi kaɗan, wasu ma su tafi ba tare da biyan komai ba.
Wata rana wani dattijo ya ce masa: “Me yasa ba ka saka farashi ba?”
Matashin ya ce: “Ina jin tsoron mutane su gudu.”
Dattijon ya ce: “Idan ka raina darajar kanka, mutane za su koya maka yadda za su raina ka.”
Tun daga wannan rana, matashin ya saka farashi, ya tsaya da gaskiya. Abin mamaki, mutane s**a fara girmama shi, kasuwancinsa ya bunƙasa.
---
Darasi
👉 Wanda bai san darajarsa jarin sa ba ya tambayi wani Dan kasuwa Daya karye yasha labari
👉 Tsoron rasa mutane wani lokaci shi ne ke sa ka rasa kanka.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano
406