Daarus-sahaabah Network

Daarus-sahaabah Network

Share

17/06/2020

KIMIYYAR HADISI A SAUKAKE

Littafi na 1 Darasi na 9

✍️ Sheikh Muhammad Auwal Nuhu Allemawy

(ci gaban bayani a kan Mashhur)

JAN HANKALI

Sau da yawa malamai kan kira hadisi da mashhuri amma ba suna nufin mushhuri na isdilahi wanda bayani ya gabata kansa ba, sai dai suna nufin shaharar hadisin a bakin mutane ko a wajan wasu nau`i na ma`abota ilimi.

Irin wannan shaharar kuwa ba ta da alaka da shahara ta isdilahi da ake bukatar mutum uku ko sama da uku su rawaito hadisi kafin ta tabbata.

Wannan shaharar da malamai kan ambata tana da alaka ne kawai da yaduwar hadisin cikin wasu nau`i na jama`a, don haka hadisin da aka siffanta da ita, na iya kasance garibi ko azizi ko mashhuri na isdilahi ko ma ya zama ba shi da isnadi kwata kwata.

Irin wannan shaharar ta kasu gida gida gwargwadon mutanen da hadisin ya shahara cikinsu.

- Akwai hadisan da sun shahara a wajan malaman hadisi. Misali: fadin Manzon Allah s.a.w:

«نضر الله امرأ سمع مقالتي فوعاها فبلغها كما سمعها»

Ma`ana: "Allah ya haskaka mutumin da ya ji maganata sai ya kiyaye ta, ya je ya isar da ita (ga wani) kamar yadda ya ji.."
Wannan hadisi ne da ya shahara a bakunan malaman hadisi, don haka idan aka kira shi mashhuri ana nufin shahara ta lugga ba ta isdilahi ba.

Amma da za mu koma ga isnadinsa za mu sa shi ne a layin hadisai mutawatirai, kamar yadda Alhafiz Assuyudy yake cewa: "wannan hadisi ne mutawatiri, kwatankwacin sahabbai talatin ne s**a rawaitoshi".

- Akwai hadisan da s**a shahara wajan malaman fikhu. Misali: hadisin:

«أبغض الحلال إلى الله الطلاق»

Ma`ana: "halalin da Allah ya fi ki shine sakin aure"

Idan da za mu koma ga isdilahi za mu ga cewa: wannan hadisi ne garibi kuma mai rauni, an rawaito shi ne ta hanyar Ubaidullahi Alwassafy daga Muharib Ibn Disar daga Abdullahi iBnu Umar.

- Akwai kuma hadisan da s**a shahara a bakin malaman nahwu kamar hadisin:

نعم العبد صهيب لو لم يخف الله لم يعصه

Ma`ana: "madalla da wannan bawa Suhaib, ko da ba ya tsoron Allah to ba zai saba masa ba"

Hadisi ne da ba

11/06/2020

Daarul Hadeethis Salafiyyah, Zaria-Nigeria.

BismilLaahir Rahmaanir Raheem...

Bayan haka:

Assalamu Alaikum wa RahmatulLaah...

Muna amfani da wannan damar wajen sanar da ɗaukacin Al'ummar Musulmi cewa za'a Tsayar da Sallar Juma'a
A *Jaami'us-Salafiy* dake muciya, haka kuma a
Daarul Hadeethis-Salafiyyah, da ke Gaskiya a gobe juma'a in shaa Allaah, sakamakon sanarwan gwamnatin jaha da ta sassuta dokar kulle sakamakon annobar covid-19.

Lokacin Sallah 12:00 na rana.

Kada a manta a sanya takunkumin rufe baki da hanci (watau: facemasks) 😷

Allaah Ya sa mudace.

11/06/2020

Allah Sarki. Ga abinda na rubuta a bara. Na dauka maganar ta wuce. Sai ga Vision FM Kaduna sun bugo mani jiya suna neman lallai a sake kara yi wa mutane bayani. Zaku saurari firar yau a wani shiri na musamman.

*Dr. Gumi da Azumin Sittu Shawwal: Magana ta Karshe*
✍ Dr. Mansur Sokoto
8 ga Shawwal 1440H (11 ga Yuni 2019)

Bismillahir Rahmanir Rahim
✒ Yau mako daya kenan da yin Sallar Idi. Kuma a kowace rana ta Allah sai wani Malami ya yi raddi kan da'awar Dr. Gumi cewa: "Azumin Sittu Shawwal bidi'a ne".
✒ Da dama daga cikin mutane sun kalli abin a matsayin sabanin Malamai ne wanda, za ka iya daukar duk maganar da ka ga dama a ciki. Wasu kuma suna kallon abin ba wata muhimmiyar magana ba ce tunda ma azumin kololuwarsa ya zama mustahabbi.
✒ Almajiran Dr suna ganin wata bajinta ce ya fito da ita inda ya kalubalanci kusan duk Malaman Sunnah, kuma ya zo da wani karatu wanda ba su da shi.
✒ Wasu da dama sun kammala azumin Sittu Shawwal a yau, wasu kuma sun fasa yi tunda yake sun gamsu cewa ba wani aikin alheri ne da Shari'a ta san da shi ba.

*Abinda nike son jawo hankalin jama'a zuwa gare shi:*
📌 Wannan magana ba ta sabani tsakanin Malamai ce ba. Domin kuwa babu wani Malami - a duk tsawon tarihin Musulunci - da ya ce, azumin Sittu Shawwal bidi'a ne in ban da Dr. Gumi. Shi kansa Imam Malik bai ce haka ba. Cewa ya yi: "Suna tsoron ya kasance bidi'a ne". Wanda ya yi nazari zai gano bambancin wannan magana da waccan. Don haka, kakaf, Malaman Malikiyya, cikin su har da wadanda s**a hardace Muwatta babu wanda ya tafi akan cewa, azumin bidi'a ne. A maimakon haka, sun yi ta nema wa Imam Malik mafita akan wannan magana, kasancewar hadisin ya tabbata daga Annabi (S) babu tantama. Kuma bai yiwuwa Annabi (S) ya yi umurni da yin abu sannan ace bidi'a ne.
📌 Malaman Sunnah sun dukufa wajen mayar da martani akan Dr Gumi ba don suna son su ci gyaransa ba. Ai Malamai har wadanda s**a fi shi suna yin kuskure kuma ayi masu uzuri. Amma shi, a nasa bangaren ba kuskure ba ne, manhaji ne ya da

Want your place of worship to be the top-listed Place Of Worship in Zaria?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

No 19 Jushin Gari
Zaria
810241