Aslam Press Foundation

Aslam Press Foundation

Share

04/09/2025

MARIGAYI ALHAJI TIJJANI YUSUF ALBARKAWA
(ALHAJI TIJJANI GYATUN)

SUNA:

Alhaji Tijjani Yusuf wanda aka fi sani da Alhaji Tijjani GYATUN.

HAIHUWA:

An haifi Alh Tijjani Yusufu ne a unguwar Albarkawa Gida mai Lamba 73, a cikin birnin Zaria a ƙarshen 1920s zuwa 1930 a ƙiyasi.

MAKARANTA:

Yayi karatu na muhammadiyya sannan kuma yayi karatu na yaƙi da jahilci

AIKI:

kafin aiki ya kasance manomi ne kamar yadda aka san ƙasar hausa, ya fara aiki a matsayin leburan asibiti a june 1963 kafin daga bisani ya samu permanent and pensionable appointment a matsayin Dresser a asibitin a September 1978. Kafin wannan appointment ya halarci training na wata shida na MEDICAL DRESSER inda ya gama a 2nd July 1977. Ya cigaba da aiki a fannin lafiya har ya kai senior community health extension worker a 1996. A yayin aikin nashi, yayi aiki a matsayin WELFARE OFFICER a Hajj operation a shekarar 1987.

GARURUWAN DA YA ZAUNA:

Yayi aiki garuruwa ƙarƙashin ƙaramar hukumar zaria kamar haka:

Zaria City
Basawa
Gadan Gayan (Igabi)

AJE AIKI:

Anyi masa ritaya a 31st May, 1998 cikin tsarin kantomar jiha na mulkin soja. bayan nan ya cigaba da harkar sa ta kwangila a wurare da dama.

ZAMANTAKEWAR SA DA MUTANE:

Ya kasance gaba gaba wajen neman ma mutane karatu musamman sashen lafiya da aiki. har ila yau ya kasance babba wajen warware dukkan matsalar da ta taso na aure, unguwa da al'amuran yau da kullum. Mai kwarjini ne kuma kowa na girmama shi

YA'YA:

Ya rasu ya bar ɗan shi ɗaya wato Yusuf Tijjani, ma'aikaci a jami'ar Bayero da ke kano

RASUWAR SA:

Ya rasu a asibitin musulmi da ke Ɗanmagaji ranar litini 26th October, 2015. Allah Ya Jaddada Rahamar Sa A Gare Shi, Ya Yafe Mashi kura kuran shi tare da sauran magabatan mu baki daya. Amin.

SHAFIN
Sabuwar Duniya

21/01/2025

Arewa Allah Ya Bamu Mafita

Want your business to be the top-listed Advertising & Marketing Company in Zaria?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

No 73 Albarkawa Zaria City
Zaria