Pi Pro Arewa
30/09/2025
Technical Analysis 101
Candlestick (6)
Single candlestick
Hammer 🔨
Hammer Candlestick 🔨
Hammer Candlestick wani shahararren Candle ne wanda Yake daga cikin Top Single Candlesticks da aka fi amfani dasu,
Sunan Hammer Candlestick ya samo asali ne daga Yanayin Siffarsa da tai k**a da Guduma 🔨
Da kuma Sakon da yake isarwa na Tashin Kasuwa,
Ma'ana idan Ka dauki Kusa ka buga mata guduma zaka kafe ta ne ta tsaya,
To k**ar Haka Hammer Candlestick yake idan ya bayyana yakan Kafe Saukar Farashi daga Saukar ya koma tashi zuwa Sama📈
Hammer Candlestick kala Biyu ne,
1) Hammer
2) Inverted Hammer
Dukansu Siffar su kusan iri 1 ce, Haka saqon da suke isarwa ma iri 1 ne,
Hammer tana zuwa ne a tsaye,
Yayin da Inverted Hammer a juye, Kanta a ƙasa,
Hammer Candlestick yana daga Cikin Bullish Reversal Candlesticks na Kasuwa, ma'ana yana cikin Candle masu juya akalar kasuwa, idan tana faduwa ta koma tashi, sak**akon Bayyanar sa,
Domin yana Nuni da Buyers Suna gab da karɓe kasuwa daga hannun Sellers domin sunci Galaba Akansu,
To Anan ne akan Samu bayyanar Hammer or Inverted Hammer 🔨 , Sai farashi ya juya daga Sauka Zuwa Tashi📈
1) Hammer Candlestick🔨 Yana Bayyana ne a DownTrend,a karshen Tafiyar Farashi.📉
Wanda yake ɗauke da sakon Tashin Farashi, 📈
2) Inverted Hammer 🔨
Shima Yana Bayyana ne a DownTrend, a karshen Tafiyar Farashi.📈
Wanda yake dauke sa sakon Tashin Farashi📈
Hammer Candlestick yana inganta ne a Yayin da Ya Fito a karshen Tafiyar Farashi, A DownTrend ✅,
Ƙarin Bayani:
Hammer Candlestick Yakan zo A kowane irin Color,
Green 🟢 or Red 🔴, indai Siffar su ya bayyana to saqon da suke isarwa, Bullish Reversal ne, Sai dai Sometimes Akan Duba sauran wasu Indicators ɗin or next Candle domin samun Confirmation before Shiga Trade,
Karin bayani Gwari-gwari 👇
Hammer da Inverted Hammer suna bayyana ne a DownTrend, wanda duka Abu 1 suke Nuni idan har s**a bayyanan,
Shine Tashin Farashi 📈
Hammer baya bayyana a UpTrend sai dai Downtrend,
shima hak
14/09/2025
Technical Analysis 101
Candlestick (5)
Single candlestick
Dragonfly Doji 2
Cigaban rubutu akan Doji candlestick.
Dragonfly Doji
Mene ne Dragonfly Doji?
Amsar:
Dragonfly doji wani candlestick ne Wanda traders suke amfani dashi wajen yin technical analysis,
Domin yin hasashen yiwuwar kasuwa tayi qasa, ko kuma ksw ta cigaba da miqewa.
Yaya wannan Candlestick na Dragonfly yake? Kuma wani features yake dashi?
Amsar:
Shidai Dragonfly doji yanda features irin na doji, shima opening price da low price da high price duk s**an kusa zuwa dai dai.
Abubuwa masu mahimmaci akan dragonfly:
A duk lokacin da wani token yayi qasa, yayin da token dinnan yake kokarin yayi recovery akan samu Dragonfly candlestick a chart din, wanda dama an riga an samu downtrend, shikuma fitowar Dragonfly yanayi maka nuni da cewa yanzu akwai potential Reversal na uptrend.
Yanaso mai analysis yasan cewa mutane sun siyar da token din sosai, ma'ana an samu selling pressure har sai da s**a tabbatar da token din yayi deep a wannan season din. Amma kuma bayan yayi deep sai kuma wasu mutane s**a dinga siyanshi har sai da s**a saka ya koma asalin farashin daya ke kafin a dumper shi. Hakan yana nufin a duk lokacin da aka ganshi a lokacin da token yayi deep, to akwai Bullish Reversal.
Ma'ana token na shirin miqewa a wannan lokacin.
Haka zalika yakan fito yayin bearish reversal.
A duk lokacin da kukaga chart ya miqe yayi sama sosai kukaga Dragonfly a saman uptrend dinnan, to hakan yana nufin akwai bearish Reversal, sbd ako wani lokaci token din zai fadi yayi qasa.
In summary:
A duk sanda kukagan chart a can qasarshi akwai Dragonfly candlestick to hakan yana nufin akwai Bullish Reversal,
Ma'ana coin yana gab da miqewa.
Haka zalika idan kunga chart yayi sama sosai kukaga Dragonfly a saman chart din to hakan yana nufin akwai bearish Reversal,
Ma'ana token yana gab da faduwa.
A taqaice kenan, hoton candlestick din yana qasa.
Click here to claim your Sponsored Listing.