Sir Wisdom II

Sir Wisdom II

Share

05/05/2026

UBANGIJINKA YANA DA ADALCI KUWA???

Wata mata ta je gurin Annabi Dauda (AS) cikin fushi, ta ce masa: "Ya Annabin Allah! Ubangijinka yana da adalci kuwa?

Sai ya ce: "Kwarai kuwa, mai adalci ne, ba ya zalunci.

Menene labarin ki? Sai ta ce: "Ni bazawara ce, ba ni da mai taimaka min, ga 'ya'ya mata guda 3 marayu. Ina ciyar da su ne da sana'anar saƙa da nake yi.

Jiya na yi sakata mai yawa, na daure a wani jan tsumma, zan tafi kasuwa na sayar, na sami abin da zanciyar da kaina da 'ya'yana, sai wani tsuntsu ya zo ya wafce daga hannuna, kuma ba ni da komai, ga marayu...😭

Kafin Annabi Dauda (AS) ya ce komai ga wannan mata, sai ga wasu mutane su 10 sun shigo, kowannen su da Dinare 100 a hannunsa, s**a ce:

"Ya Annabin Allah! Muna son za mu yi sadaka da wannan kudi, Sai Annabi Dauda (AS) ya ce da su: "Me ya faru?" Sai s**a ce:
"Muna cikin jirgin ruwa, sai iska mai karfi ta taso, jirgin namu ya bule, sai muka dinga ambaton Allah, kuma muka yi bakancen idan Allah Ya tseratar da mu, za mu yi sadaka da Dinare dari-dari.

Muna cikin wannan hali, sai wani tsuntsu ya jeho mana wani jan tsumma, a cikin tsumman akwai wata saƙa.
Sai muka toshe bular da wannan saƙar, Allah Ya tseratar da mu.

Sai Annabi Dauda (AS) ya yi godiya ga Allah, ya fuskanci wannan mata ya ce mata: "Ubangijinki mai adalci ne... Idan kin yi saƙar nawa k**e siyarwa?"

Sai ta ce: "Dirhami daya".
Sai ya ce: "Ga Dinare 1000, Allah Ya sayi saƙarki, karbi ki je ki ciyar da 'ya'yanki".

ya ubangiji ka warware mana matsalolin mu, ka yalwata arzikin mu 🙏🙏

Sir Wisdom II pen...🖊️

Want your school to be the top-listed School/college in Zaria?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Zaria