JASAM MEDIA ZARIA UNITL
31/08/2022
*ZIYARAR JAISHI AMIRUL MUMININ A GARIN ZARIYA.*
Jaishu amirul mu'umineen sun shirya ziyara a birnin Zariya domin ta'aziyya da duba marasa lafiya da sauran wasu wurare acikin garin zariya.
Na farko Jaishi amirul mu'umineen sun fara kai ziyara ne asbiti inda shahidai masu rai suke jinya tun waki'ar da akayi a ranar ashura, Anziyarci shahidai masu rai sannan an musu addu'a akan Allah ya basu lafiya sannan aka dan musu jawabi atakaice,sannan muna cikin Asibitin sai ga wasu shahidai masu rai wayanda aka samu a waki'ar soba ta ranar lahadi 28/08/2022.
Bayan futowa daga Asibitin aka dunguma gurin shekh abdulhamid bello a gidan sa wanda yayi nasihar falalar shahada, aikin da ya rayata akan matashi wanda yake dan gwagwarma ya, falalar ziyara a muslumci, a karshe ya kara tunatar damu hadafin wannan Harkan (Neman yardan Allah).
Bayan futowa daga gidan malam Abdulhamid bello aka nufi gidan sayyid badamasi kanin jagoranmu sayyid Zakzaky (H). Da farko yayi jawabi me ratsa jiki akan dukkan hanyar Allah, Sannan yayi jawabi akan falalar shahada, a karshe azzalumai masu kisan kai susan cewa da jinin shahidai addinin Allah ze tabbata a karshe aka Karrama shi da zanen photon shahid muhsin.
Bayan nan Anziyarci makwanciyar mahaifiyar jagoran mu sayyid Zakzaky (H) da yake unguwar jushi ziyarar an gabatar da addu'oi.
Akarshe an ziyarci darur-rahma makwancin shahidan mu innalillahi wa inna ilahir rajiun, anan ne muka ziyarci Yayan jagoran mu sayyid Zakzaky (H) sayyid Ahmad, sayyid Mahmud, sayyid Hameed, sayyid muhsin, da sauran shahidan harkan musulunci.
Allah subahanahu wata ala ya kara wa jagoran mu lafiya ya cika masa burin sa, mukuma ya tabbatar damu akan aikin mu na harisanci
*JAISHI AMIRUL MUMININ (AS) MEDIA*
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Culinary Team
Attire
Contact the university
Telephone
Website
Address
Zaria
@#$%&-+()